Mutum 6 da aka sace a Taraba sun kai wata biyu a tsare yanzu

Mutum 6 da aka sace a Taraba sun kai wata biyu a tsare yanzu

- Al'ummar jihar Taraba na cigaba da juyayin yan uwansu mutum shida da aka sace tsawon wata biyu kenan yanzu babu labarinsu

- Mutanen da aka sacen sun hada da yan mata biyu, wani lauya da masu kiwon shanu uku wanda aka sace a Kofan Amadu dake tsakanin Wukari da Takum a jihar Taraba

Wasu mutane shida da aka sace a Taraba sun kwashi tsawon wata biyu a hannun magauta ba tare da an san inda suke ba.

Wadanda aka sacen sun hada da yara mata biyu, lauya daya da kuma makiyaya shanu guda uku. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa iyalan wadanda aka kama na cike da bakin ciki kan rashin sanin halin da yan uwansu ke ciki.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa iyalan yan matan biyu basu ji daga wurin yaran bat un lokacin da aka sace su yanzu tsawon wata biyu kenan.

Masu garkuwan su nemi a biyasu N15m a matsayin fansar lauyan sai dai iyalansa sun bada N1.5m wanda yan ta’addan suka ki karba.

KU KARANTA: Obasanjo ya tambayi Buhari kan isalin sayen gidan sauro

Shi kuwa mahaifin makiyayan uku dake hannun masu garkuwan yaki amincewa da biyan kudin fansa domin yaransa.

Bayan an dauki tsawon wata biyu tun lokacin da masu garkuwar su kayi gaba da wadannan mutanen tsit kake ji kan makomar wadanda aka sacen. Hakan ya haifar da shakku da kuma firgici tsakanin iyalan nasu.

Dukkanin wadannan mutanen dai an kama su ne kan hanyar Kofan Amadu wacce ke tsakanin Wukari zuwa Takum.

Bincikenmu ya nuna mana cewa hanyar ta yi kaurin suna wurin sace-sacen mutane inda aka sace mutane da yawa cikin watannin da suka gabata, kana da yawa daga cikinsu na hannu har ila yau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel