Abba Gida-Gida na zargin INEC da shirya masu gadar zare

Abba Gida-Gida na zargin INEC da shirya masu gadar zare

Dan takarar jam’iyar PDP a zaben gwamnan Kano da ya gabata Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa bisa ga tsaiko daga bangaren hukumar INEC akan hana jam’iyarsa ta binciki kayayyakin da akayi aiki da su wurin zabe.

Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida yace hukumar zaben ta kirkiri wannan tsaikon ne da gan-gan saboda tana son ta hana jam’iyarsu hakkinta na bincikar kayayyakin zaben.

DUBA WANNAN:Buhari bai amince da samar da 'yan sandan jiha ba - Fadar Shugaban kasa

Yayi wannan furucin ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai a babban ofishin INEC dake Kano inda ya tafi domin ya samo dalilin tsaikon da ake samu, amma sai dai bai tadda jami’in hukumar ko daya ba a ofis wanda zai iya sauraron korafin da ya zo da shi.

“Idan baku manta tun daga lokacin da muka shiga kotu, mun nemi a bamu dama domin yin binciken kayayyakin zaben da hukumar INEC tayi amfani da su wurin gudanar da zaben gwamna. Amma sai dai tun a wancan lokacin har yanzu abin na tafiyar hawainiya.” Inji shi.

“ Bugu da kari akwai izini daga kotu cewa hukumar ta bamu bugun takardun da akayi amfani da su sai dai hakan ya ci tura. Hukumar ma korarmu sukayi daga harabar ofishin na su tare da cewa mu koma kotu a sake bamu wani izinin domin wa’adin da aka bamu a yanzu ya riga da ya kare.” A cewarsa.

“ Ba mu san me INEC ke kitsawa ba, jan lokacin nasu yayi yawa. Ba mamaki tana shirya wani ha’inci ne domin ta sauya dukkanin kurakuranta kana ta juya ainihin abinda kenan zuwa akasin haka wanda zai tabbatar da APC bata sauka a mulkin ba.” Inji Abba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel