Karyar shekaru: NYSC zata sanya shekarar haihuwa a kan shahadarta

Karyar shekaru: NYSC zata sanya shekarar haihuwa a kan shahadarta

-Hukumar NYSC zata fara sanya shekarun haihuwa akan shahadar kammala bautar kasa, inji shugaban hukumar.

-A cewar shugaban wannan matakin ya zama dole a garesu saboda wasu daga cikin jami'o'in kasar nan na turowa zuwa ga hukumarsu mutanen da shekarunsu sun wuce tafiya bautar kasan.

Shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim yace hukumarsa zata fara sanya shekarun haihuwa akan shahadar kammala bautar kasa ta.

Shugaban yace wannan sabon tsarin ya zama wajibi a garesu duba ga yawan kirkirar shekarun karya da ya zama ruwan dare a tsakanin daliban dake shirin tafiya bautar kasa bayan kammala karatun jami’a.

Karyar shekarun haihuwa: NYSC zata sanya shekarar haihuwa a kan shahadarta

Karyar shekarun haihuwa: NYSC zata sanya shekarar haihuwa a kan shahadarta
Source: UGC

KU KARANTA:Da duminsa: Masu dukiya sayen shari’a sukeyi a Najeriya -Lawan

Shugaban ya sanar da wannan maganar ne a Abuja yayin da ake gudanar da wani taron wayar da kai akan tawagar masu bautar kasa kasha na biyu a 2019 wato Batch B.

A cewarsa wannan matakin yazo daidai lokacin da hukumar ke kokarin fidda bara gurbi daga cikin masu shirin tafiya bautar kasar da jami’o’i ke turowa ga hukumar, inda yace akwai wadanda shekarunsu ya wuce na zuwa bautar kasan.

“ Mun gama bincike mun gano cewa wasu makarantun na bamu mutanen da sun riga sun tsufa da zuwa wajen bautar kasa. Irin wadannan daliban suna rage shekarunsu ne domin guje ma takardar rashin tafiya bautar kasan.

“ Hukumar mu baza ta amince da irin wannan danyen aiki na son rai ba, duk makarantar da muka samu da hannu cikin irin wannan aiki to lallai zata fuskanci hukunci mai tsauri.

“ A yinkurinmu na dakatar da karairayin shekarun haihuwa, zamu fara sanya shekarar haihuwa dauke a kan shahadar kammala NYSC da muke ba duk wanda ya kammala bautar kasar a karshen shekararsa ta bautar kasan.” Inji Shuaibu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel