Za’a rantsar da Buhari tare da gwamanoni 29 a yau

Za’a rantsar da Buhari tare da gwamanoni 29 a yau

-A yau Laraba ne za'a rantsar da shugaba Buhari a wa'adinsa na biyu domin mulkin Najeriya.

-Gwamnonin jihohi 29 ne zasuyi rantsuwar karbar ragamar mulki a yau dina nan, daga cikinsu 12 ne kadai sabbi yayin da 17 daga cikinsu tsoffin gwamnoni wadanda zasu koma wa'adi na biyu akan mulkin.

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo tare da gwamnoni 29 da mataimakansu za suyi rantsuwa domin karbar ragamar mulki a yau din nan.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa wasu daga cikin gwamnoni masu barin gado sun riga da sun mika takardun murabus ga wadanda zasu maye gurabensu tun tuni.

Za’a rantsar da Buhari tare da gwamanoni 29 a yau

Shugaba Muhammadu Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:INEC ta fara bitar zabukan 2019

Shugaba Buhari tare da mataimakinsa Osinbajo za’a rantsar dasu yau a Eagle square dake Abuja domin shiga zango na biyu na mulkinsu.

Shugaba Buhari shine yayi nasarar lashen zaben shugaban kasa inda ya kada yan takara daga jam’iyun siyasa 73 ciki hadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyar PDP a zaben 23 ga watan Fabrairun 2019.

Gwamnoni 12 ne sabbi daga cikin 29 da za’a rantsar a yau, wannan rantsuwar ita ce ta farko a garesu a matsayin gwamnonin jihohi. Yayin da sauran 17 kuma zasu koma ne a wa’adi na biyu bayan sun yi nasarar lashe zaben 9 ga watan Maris.

Dukkanin gwamnoni sun fito ne daga jam’iyun APC da PDP cikin jam’iyun siyasa 90 da suka fafata a zaben da ya gabata.

Sabbin gwamnoni sun hada:

Umaru Fintiri (PDP, Adamawa),

Babagana Zulum (APC, Borno),

Bala Muhammad (PDP, Bauchi),

Inuwa Yahaya (APC, Gombe),

Emeka Ihedioha (PDP, Imo),

Babajide Sanwo-Olu (APC, Lagos),

Dapo Abiodun (APC, Ogun),

Seyi Makinde (PDP, Oyo),

Abdulrazaq AbdulRahman (APC, Kwara),

Abdullahi Sule (APC, Nasarawa),

Mai-Mala Buni (APC, Yobe) da kuma

Bello Mutawalle (PDP, Zamfara).

Sauran jihohin kuwa gwamnoninsu ne zasu sake komawa kan ragamar mulkin wanda suka kunshi jihohin, Abia, Ebonyi, Enugu, Akwa Ibom, Cross River, Delta, Rivers, Filato, Binuwe, Neja, Taraba, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa da Sokoto.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel