Madalla: Yan sanda sun kama yan ta’adda 71 a Kaduna

Madalla: Yan sanda sun kama yan ta’adda 71 a Kaduna

-Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna ya bayyanawa manema labarai gagarumar nasarar da rundanarsa ta samu a cikin makonni uku da suka shude inda tayi nasarar damke yan ta'adda mutum 71.

-Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Ali Janga shi ya fadi wannan batu da kansa yayin wata tattaunawa da yayi da yan jarida a ofishinsa ranar Talata.

A ranar Talata ne rundunar yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu nasarar damke mutane 71 cikin makonni uku da suka gabata wadanda ake zarginsu da aikata miyagun laifuka iri daban daban.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ali Janga shi ne ya shaidawa manema labarai wannan batu a babban ofishin hukumar dake jihar Kaduna.

Madalla: Yan sanda sun kama yan ta’adda 71 a Kaduna
CP Ali Janga, kwamishinan yan sandan Kaduna
Asali: Facebook

KU KARANTA:Basaja da aikin kwastam: An yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara 5

Janga, yace ya zama wajibi a gare shi na ya sanar da yan jarida ayyukan da rundunarsu keyi da kuma cigaban fagen yaki da ta’addanci tare da sauran miyagun laifuka a jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa mutanen 71 da aka kama an damkesu ne akan laifuka daban daban wadanda suka hada da, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma laifin kisan kai.

Bugu da kari, daga cikinsu akwai wadanda aka kama da laifin mallakar muggan makamai, kwayoyi da sauran ababen da aka haramtawa jama’a mallakarsu bisa dokar kasa.

Kazalika ana zargin yan ta’adda da laifin shaye-shaye, fasa shaguna domin yin sata da kuma kafa kungiyoyin yan daba masu fitinar mutane.

Kwamishinan ya fadi wasu daga cikin ababen da aka samu a wurin wadannan mutane, daga cikin kayayyakin akwai bindiga kirar dobul barel, motar bas kirar Toyota mai dauke da lambar XB 119 SMN da kuma Toyota kirar Hilux mai dauke da lambar BRK 901 AA.

Har ila yau, akwai motoci biyu kirar Gwalf, Toyota korola guda 3 da kuma Honda kirar EOD dauke da lambar ABC 846 GP. An kuma same su da layu, wukake, akwatin talabijin da kwayar Diazepam.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel