Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

A daren ranar Litinin, 27 ga watan Mayu ne, aka yi wata hira ta musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce aka nuna kai tsaye da a gidajen Talabijin da Radiyo da sauran kafafen watsa labarai dake fadin Najeriya.

'Yan jaridu sun yiwa shugaba Buhari tambayoyi da dama a kan al'amuran da suka shafi kasa da kuma mulkinsa a zango na farko da kuma irin shiri da manufofi da yake da su a zangon mulkinsa na biyu da za shiga.

Ga wasu muhimman abubuwa 10 da shugaba Buhari ya fada yayin hirar da aka yi da shi:

1. Tun kafin a gudanar da zabe na san nine zan yi nasara

2. Na samu nasara a yaki da Boko Haram. Kafin na hau mulki, sune keda iko da kananan hukumomi 17 a jihar Borno.

3. Zan tabbatar da cewar rundunar 'yan sanda da bangaren shari'a sun cigaba da daukan tsaurararan matakai a kan 'yan ta'adda

4. Na yi bankwana da majalisar zartar wa da na kafa. Ban tattauna da kowa ba dangane kunshin sabbin ministocin da zan nada.

Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi

Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya fada yayin hira da shi
Source: Twitter

5. Mun kwato dukiya mai yawa daga hannun wadanda ake tuhuma da laifukan cin hanci. Akwai bukatar taka tsan-tsan a kan harkar yaki da rasha wa, ba abin sauri bane.

6. A kan nadin shugabannin hukumomin tsaro, shugaba Buhari ya ce; "na yi dogaro da bayanan su na aiki ne kafin na nada su."

DUBA WANNAN: Zan bawa masu kira na 'Baba Go slow' mamaki a zango na biyu - Buhari

7. A kan alakar sa da majalisa, shugaba Buhari ya bayyana cewar; "dole a samu matsala duk lokacin da bangaren majalisa suka fara jin daidai suke da bangaren zartar wa. Na taba taba tambayar Bukola a kan menene ribar sa a cin dunduniyar gwamnati. Na dade da saka shi cikin marasa kishin kasa."

8. Buhari ya bukaci 'yan Najeriya su tona asirin duk wasu masu laifi da marasa gaskiya dake kusa da su

9. "Masu kira na da 'Baba go slow' zasu sha mamaki a wannan karon" a cewar Buhari

10. Majalisa bata da wani uzuri na rike kasafin kudi har tsawon watanni bakwai

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel