Matasan Najeriya akwai hazaka kwarai da gaske, inji Buhari

Matasan Najeriya akwai hazaka kwarai da gaske, inji Buhari

-Dan takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 ya yabawa matasan Najeriya inda yace su ba ragwaye bane.

-Ahmed Buhari yayi wannan furucin ne wurin wani taro na musamman mai taken 'Ni dan Najeriya ne' da aka shirya domin yara masu tasowa.

Dan takara mafi karancin shekaru wanda ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a zaben 2019, Ahmed Buhari shine yayi wannan furucin cewa matasan Najeriya ba ragwaye bane.

Yayi wannan kalamin ne a jiya Juma’a wurin wani taro na musamman mai taken ‘Ni dan Najeriya ne’ wanda wata kungiya mai suna Project One Productions ta shirya.

Matasan Najeriya akwai hazaka kwarai da gaske, inji Buhari

Matasan Najeriya akwai hazaka kwarai da gaske, inji Buhari
Source: UGC

KU KARANTA:Kurun kus! gaskiya tayi halinta a jihar Zamfara, inji Atiku

Taron wanda ya maida hankali akan zakulo kwazon yan Najeriya musamman wadanda ke da ilimi domin da su ne kadai kasarmu zata iya alfahari da su.

A cewar Buhari, “ Duk sanda ka zauna da abokanka na kasar waje ka fada masu matsalar kasarku, girman da suke baka dole zai ragu. Matasan Najeriya ba ragwaye bane.

“ Duk yadda matsalar mutum ta kai da lalacewa ba’a kashe mashi karfin gwiwa karfafa shi ya dace kayi. Saboda komi yayi farko tabbas yanada karshe, bayan wuya kuma sai dadi.

“Nasara na samuwa ne kadai ta hanyar jajircewa da kuma mu’amala tare da abokai masu son cigaba da kuma taimakon juna da shawarwari nagari. ‘Ni dan Najeriya ne’ an kaddamar da shi ne domin samar da cigaba, bamu fara don mu bari ba.”

Da take nata jawabin wacce ta fito da wannan tsari, Misis Bisayo Busari Akinnadeju tace, “ Iya tsawon tunanina na dade ina son ganin na hada kan Najeriya a bangaren kawo cigaba. Najeriya wacce zamuyi alfahari da ita ba tare da duban bambancin addini, kabila ko jinsi ba. A don haka ne na fito da wannan shiri na ‘Ni dan Najeriya ne’ wanda ya kunshi kowa da kowa.”

“ Kamar yadda Nelson Mandela yace, babu al’ummar da zata samu abinda ya kamaceta idan bata baiwa yaranta kulawa mai kyau ba. Hakika na aminta da maganarsa dari bisa dari, ko ba komi dai yara sune manyan gobe.” Inji misis Bisayo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel