Rikicin manoma da makiyaya: Najeriya na asarar $13bn ko wace shekara a yankin Arewa ta tsakiya, inji kasar Amurka

Rikicin manoma da makiyaya: Najeriya na asarar $13bn ko wace shekara a yankin Arewa ta tsakiya, inji kasar Amurka

-Kasar Amurka ta koka akan rikicin manoma da makiyaya dake addabar yankin arewacin Najeriya wanda ke sanadiyar asarar $13bn a ko wace shekara.

-Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya fitar da bayanai dake nuna cewa cikin shekaru 5 rikicin yayi sanadiyar mutuwar mutum 7000 da kuma asarar tattalin arzikin kasar.

Kasar Amurka tace Najeriya na tafka asarar kudin da yawansu ya kai $13bn a kowace shekara saboda ricikin manoma da makiyaya da ya addabi yankin Arewa ta tsakiya.

Jawabai da dama na nuna cewa kimanin mutane 7000 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru biyar da suka wuce a wannan yanki sakamakon rikicin.

Rikicin manoma da makiyaya: Najeriya na asarar makudan kudade a yankin Arewa ta tsakiya, inji kasar Amurka

Rikicin manoma da makiyaya: Najeriya na asarar makudan kudade a yankin Arewa ta tsakiya, inji kasar Amurka
Source: Twitter

KU KARANTA:EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

Yankin arewa ta tsakiya ya kunshi jihohin Binuwe, Filato, Nasarawa, Neja da kuma wani sashe daga cikin jihar Kaduna wanda cikin ‘yan shekarun nan ke fama da rikice-rikice daban daban.

A wani zance da ya fito daga ofishin jakadancin kasar Amurka dake Abuja, ya nuna mana cewa kimanin mutum 7000 ne suka mutu cikin shekaru 5 yayin da tattalin arziki ke samun nakasun $13bn a kowace shekara.

“ A shekara hudu da suka wuce, hukumar kula da cigaban kasashen duniya ta Amurka wato (USAID) ta fitar da wani tsari domin wanzar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya dake yankin Arewa ta tsakiya.

“Wannan tsari ya taimaka kwarai da gaske wurin farfado da martabar wuraren da rikicin ya shafa musamman a jihohin Binuwe da Nasarawa.” A cewar ofishin jakadancin Amurka.

Kazalika, kasar Amurka na kallon wannan al’amari a matsayin matsalar da yakamata a ce an maganceta tun tuni. Amma sai ga shi wankin hula ya kai Najeriya dare, a sanadiyar hakan an rasa rayuka da dama da kuma dukiyoyi saboda rikicin ya girmama ne inda ya yadu zuwa wurare da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel