Shugabancin majalisa: Zababben gwamnan Yobe ya mara wa Ahmad Lawan baya

Shugabancin majalisa: Zababben gwamnan Yobe ya mara wa Ahmad Lawan baya

Mai Mala Buni, zababben gwamnan jihsar Yobe, ya roki mambobin majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da su tsayar da dan takara Sanata Ahmad Lawan a mukamin shugaban majalisa.

Zababben gwamnan ya bayyana rokon nasa a ranar Litinin a hira ta wayar tarho da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Damaturu.

Ya bayyana cewa Lawan, wanda ya zama sanata a 2007 mai wakiltan yankin Arewacin Yobe, ya nuna kwarewa, biyayya, jijircewa da bauta duk wadanda aka san shugaba nagari dasu.

Shugabancin majalisa: Zababben gwamnan Yobe ya mara wa Ahmad Lawan baya
Shugabancin majalisa: Zababben gwamnan Yobe ya mara wa Ahmad Lawan baya
Asali: Depositphotos

Mai Mala yace shawaran jam’iyyar akan tsayar da Lawan ya kasance don tabbatar da fahimta tsakanin majalisar dattawa da majalisar zartarwa don gudanar da ayyukan cigaba da inganta rayukan yan Najeriya.

“Basiran dake tattare da tsayar da Lawan da jam’iyyan tayi a mukamin shugaban majalisa kokari ne na gudun maimaita kuskure wajen kafa shugabancin majalisa don tsare yancin yan Najeriya da damukardiyya.

KU KARANTA KUMA: Kalli bidiyon yadda yan sanda suka kakkabe maboyar yan bindiga a Katsina

“Baza mu amince da kasancewa jam’iyya mai mulki ba, sannan mu kasance da rababbun gida ba, kamar yanda muka fuskanta a shekaru hudu da suka gabata."

Ya kuma yaba ma masu ruwa da tsaki a jam’iyyar akan goyon bayan tsayar da Sanata Lawal.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel