Anyi sulhu a tsakanin Hadiza Gabon da Nabraska bayan ta roke shi

Anyi sulhu a tsakanin Hadiza Gabon da Nabraska bayan ta roke shi

Rahotanni sun kawo cewa anyi nasarar sasanta tsakanin fitacciyar jarumar nan ta Dandalin Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon da abokin sana’arta Mustapha Nabraska.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Nabraska ya yafe wa Gabon akan karar da ya shigar gaban kotu bayan ta duka gwiwa bibbiyu ta nemi yafiyarsa a harabar kotu a ranar Litinin, 20 ga watan Mayu.

An tattaro cewa j ami’an ‘yan sanda sun kamo jarumar a jihar Kaduna bayan da kotun majistare da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin kamo ta saboda kin amsa gayyatar kotun da ta yi.

A zaman da aka yi a yau Litinin, lauyan Gabon ya shigar da roko ga kotu ne kan ta janye shari’ar tunda dai an samu yin sulhu tsakanin wadanda ke rikicin kuma ta roke shi, ya yafe ma ta.

Daga nan sai Mai shari’a Muntari Dandago ya ja kunnen jarumar a kan kin amsa gayyatar kotu da ta yi, ya na mai cewa, babu wani mutum a kasar da ya fi karfin kotu ta gayyace shi, ballantana ita.

Anyi sulhu a tsakanin Hadiza Gabon da Nabraska bayan ta roke shi
Anyi sulhu a tsakanin Hadiza Gabon da Nabraska bayan ta roke shi
Asali: Instagram

Ya bada misalin cewa, shugaban majalisar dattawa na kasa da babban sufeton ‘yan sanda da makamantansu ma sun amsa gayyatar kotuna daban-daban.

Daga nan sai ya yi yanke hukuncin cewa, nan da shekara guda idan a ka kara jin ta ko ganin ta ta yi ko harara ga Jarumi Nabraska, to kotu za ta kamo ta kuma ta hukunta ta.

KU KARANTA KUMA: INEC ta janye takardun shaidar cin zabe na yan takara 25

a baya Legit.ng ta ruwaito cewa Jarumi Mustapha Naburaska ne ya shigar da kara a kotu kan zargin cin zarafinsa da barazana da ya ce da Hadiza Gabon din ta yi masa.

An tattaro cewa Naburaska ya shigar da kara a kotu ne kai tsaye saboda yana fargabar 'yan sanda ba za su dauki mataki a kan ta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel