Noma tushen arziki: Manoman shinkafa zasu samu tallafi daga wurin gwamanati

Noma tushen arziki: Manoman shinkafa zasu samu tallafi daga wurin gwamanati

-Gwamnati tarayya zata bada tallafin yin noma a karo na biyu

-Wannan tallafin ya ta'allakane zuwa ga manoman shinkafa, kamar yadda shugaban kungiyar manoma shikafan a Daura ya fadi

Sama da mutum 1,108 wadanda suka fito daga karamar hukumar mulkin Daura ta jihar Katsina ne zasu amafana da tallafin noma wanda gwamnatin tarayya ke bayarwa a karo na biyu. Akasarin wadannan mutane dai manoma shinkafa ne.

Mallam Nura Baure shugaban kungiyar manoman shinkafa ta kasa wato RIFAN reshen jihar Katsina, ne ya bayyana wannan maganar ga kamafanin dillancin labarai na kasa wato NAN.

Noma tushen arziki: Manoman shinkafa zasu samu tallafi daga wurin gwamanati

Noma tushen arziki: Manoman shinkafa zasu samu tallafi daga wurin gwamanati
Source: UGC

KU KARANTA:Wasu gwamnoni na shiga sharo ba shanu a jihohinsu, inji Dogara

Shugaban kungiyar manoman shinkafan yace, “ dukkanin wani shiri na bayar da tallafin an riga da an kammala shi a yanzu.

" Ko wane manomi za’a bashi injimin ban ruwa domin noman rani, takin zamani, maganin kwari, dan feshi da kuma irin shinkafa a matsayin bashi wanda zasu biya bayan shekara daya".

Baure yayi karin haske inda yake cewa, kimanin manoma 5,800 ne zasu amafana da wannan tsarin na tallafawa karo na biyu. Tantancewar da ake kanyi a yanzu ta manoman itace zata bada damar sanin girman filin mutum da kuma irin kayayyain da za’a bashi.

Shugaban yace kwanan nan za’a tura da wadanda suka karbi tallafin a karon farko amma har yanzu sun ki biya. Bugu da kari, Nura yace a karkashin ofishinsa wadanda suka karbi bashi tuni suka fara biya ba tareda bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya tabbatar mana cewa sama da manoma 2,500 ne suka amfana da wannan tallafi a karamar hukumar Daura, tun daga lokacin da aka kaddamar dashi a shekarar bara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel