Duniya ina zaki damu: Anyiwa wata yarinya ‘yar shekara 5 yankan rago a Kebbi

Duniya ina zaki damu: Anyiwa wata yarinya ‘yar shekara 5 yankan rago a Kebbi

-Wasu mutanen da ba'a san ko su waye ba sunyiwa wata yarinya 'yar shekara 5 yankan rago a jihar Kebbi

-Yarinyar na bacci tare da kakarta yayinda wannan iftila'i ya akfa mata

Wata yarinya ‘yar shekara 5 da haihuwa ta hadu da ajalinta ta yayinda aka yi mata yankan rago a karamar hukumar Zurun jihar Kebbi.

Yarinyar wacce aka shimfideta bisa tabarma domin ta sha iska saboda zafi a unguwar Rikoto, anyi awon gaba da ita ba tareda an san mutanen da sukayi mata wannan abin ba, kamar yadda makwabtan iyayenta suka fadi.

Duniya ina zaki damu: Anyiwa wata yarinya ‘yar shekara 5 yankan rago a Kebbi

Duniya ina zaki damu: Anyiwa wata yarinya ‘yar shekara 5 yankan rago a Kebbi
Source: UGC

KU KARANTA:Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil

Wakilin jaridar Daily Trust wanda ya samu zantawa da kakar yarinyar ya sanar damu cewa, a daidai lokacin da kakar wacce ke bacci ta farka ta ga babu yarinyar kusa da ita, sai ta fasa ihu tana neman agaji.

“ Yayinda sukaji kakar na ihun kiran sunan yarinyar sai suka yi jifa da ita suka gudu, bayan da sun riga da sun yankata.” A fadar wani makwabcinsu.

Kazalika mazaunan wannan unguwa sun bazama domin neman wadanda suka tafka wannan aika-aika sai dai yinkuri nasu ya zama na banza saboda ko keyarsu basu gani ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamarin. “ Har yanzu dai bamu kama ko mutum guda ba, amma muna kan binciken lamarin.” Inji kakakin rundunar yan sandan jihar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel