Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil

Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil

-Jama'ar karamar hukumar Wudil sunyi mubaya'a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil

-Babu abinda zamu cewa gwamnatin Kano sai godiya, inji Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa

Wata kungiya dake zaune a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano tace tana matukar murna da sabbin masauratun da gwamnatin jihar Kano ta nada a yanzu, inda kungiyar ta kara da cewa kungiyarsu da kuma ilahirin jama’ar karamar hukumar Wudil sunyi mubaya’a ga masarautar Gaya.

A wata takarda wacce ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa da kuma sakatarensa Alhaji Audu Sale Utai ne muka samu wannan labari.

Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil
Sabbin masarautun Kano: Munyi mubaya’a ga masarautar Gaya, inji wata kungiya dake Wudil
Asali: UGC

KU KARANTA:Nadin sarautar da kayi haramtacce ne - Kotu ta fada wa Ganduje

A cewar takardar jama’ar Wudil na mika godiyarsu ga gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da majalisar dokokin jihar na kirkirar wadannan masarautun guda hudu.

Kari akan abinda takardar ke kunshe dashi, shine tayi bayani akan cewa hakan zai kara bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma lamuran siyasa na Wudil ta karkashin masarautar Gaya.

“ Bayan tattaunawar tsawon lokaci, kungiyar da mutanen karamar hukumar Wudil sunyi mubaya’a zuwa ga wannan sabuwar masarauta wacce ke Gaya. Kuma jama’ar wannan yanki zasu cigaba da yin abinda zai kawo cigaba a karamar hukumar Wudil, jihar Kano da kuma Najeriya baki daya.” A cewar takardar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel