Majalisar dattawa taci alwashin dakatar da kamfanin Bet9ja

Majalisar dattawa taci alwashin dakatar da kamfanin Bet9ja

-Kwamitin matasa da wasanni na majalisar dattawa ya lashi takobin rufe kamfanin caca na Bet9ja idan har yaki amsa gayyatarsu

-Kwamitin ya riga da ya aikawa kamfanin goron gayyata a karo na farko inda kwamitin ke cewa rashin amsa gayyatar a karo na biyu zai haddasa hukunci mai tsauri

Kwamitin matasa da wasanni na majalisar dattawa yaci alwashin rufe kamfanin Bet9ja idan har kamfanin ya ki bayyana a gaban kwamitin a karo na biyu.

Shugaban wannan kwamiti, Obinna Ogba yayi wannan furuci lokacin da suke tantance kamfanonin buga caca dake aiki a Najeriya.

Majalisar dattawa taci alwashin dakatar da kamfanin Bet9ja

Majalisar dattawa taci alwashin dakatar da kamfanin Bet9ja
Source: Facebook

KU KARANTA:Bankwana da mulki: Saraki ya bukaci hadimansa su rubuta takardar ajiye aiki

Yace rashin halartar kamfanin zuwa wurin tantancewa abu da ya bamu mamaki saboda ko kadan basuyi tsammanin hakan ba.

Yayinda ya bukaci hadiminsa day a sake aikawa kamfanin da wata gayyata, sanatan ya fadi cewa “ Idan har suka ki amsa gayyatarmu a wannan karo tabbas zamu rufe kamfaninsu.”

Ya kara da cewa an shirya wannan taron tantancewa ne biyo bayan korafe-korafe daga bakin kamfanonin cacar kasar nan.

Wasu daga cikin masu wannan sana’a basu da ofishi idan kuma wasu sun kasance suna yin wannan sana’a ba tareda biyan gwamnati hakkinta ba.

Kimanin kamfanoni guda 20 suka bayyana gaban kwamitin a ranar Talata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel