Yan bindiga sun kashe jami'an JTF 6 a Zamfara

Yan bindiga sun kashe jami'an JTF 6 a Zamfara

-Yan bindiga sun kashe mutane 6 a wani harin da suka kai karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara a ranar Lahadi

-Dambazau yayinda ya ziyarci yankin yace gwamnati bata ga ta zama ba har sai ta ga bayan masu tayarwa mutane hankali a wadannan yankunan

A ranar Lahadin da ta gabata ne yan bindiga suka kai samame karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara inda suka kashe jami'an JTF mutum 6, kamar yadda mataimakin shugaban karamar hukamar Sani Galadima ya fadi.

Galadima yayi fashin baki akan lamarin ne yayinda ministan tsaron cikin gida wato Abdurrahman Dambazau ya kai wata ziyara jihar Zamfara a cigaba da kokarin gwamnatin tarayya na ganin an kawo karshen matsalar.

Yan bindiga sun kashe mutum 6 yan JTF a Zamfara
Yan bindiga sun kashe mutum 6 yan JTF a Zamfara
Asali: Depositphotos

KU KARANTA:Sanatan Kaduna ya maidawa Shugaba Buhari martani a game da batun Digiri

“ Yan bindiga sun kashe yan kungiyar JTF mutum 6 a ranar Lahadin da ta wuce a daidai kan hanyarsu ta komawa gida bayan su karbi albashinsu a Shinkafi.” Inji Galadima.

“ Ko jiya hakimin Shinkafi ya samu wasika daga wurin yan bindigan inda suke cewa zasu kawo samame garin na Shinkafi.

“ Wannan abu sam ba dadi gaskiya, a kulliyaumin muna biyan kudin fansa zuwa ga wadannan mutane yayinda sukayi garkuwa da jama’armu. Muna bukatar agajin gaggawa daga wurin gwanmati domin kawo karshen wannan matsalar.” Inji mataimakin shugaban karamar hukumar.

Da yake nashi jawabin, Dambazau yace ya ziyarci karamar hukumar Anka inda nan ma yaje ne domin tattaunawa da masana sha’anin tsaro a jihar ta Zamfara.

Ya sake cewa shugaba Buhari ya damu kwarai akan tabarbarewar tsaron jihar Zamfara. “ Wannan bashi bane zuwanmu na farko jihar Zamfara, mun dau tsawon lokaci da daukar wannan mataki domin magance rashin tsaro bama a Zamfara kadai ba.

“ Shugaban kasa ne ya umurceni da in tafi Anka da Shinkafi domin tattaunawa da sarakunansu akan wadannan matsaloli. Kana kuma yace inyi maku jaje a madadinsa bisa abubuwan dake faruwa a yankunanku.

“ Wajibin gwamnatine ta tabbar da kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a. A don haka ya zama dole a matsayinmu na gwamnati mu kawo karshe wannan matsalar.” Inji Dambazau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel