Ramadan: Ku yi taka tsan-tsan da nau’in abincin da kuke ci, Likita ya shawarci masu ciwon gyambon ciki

Ramadan: Ku yi taka tsan-tsan da nau’in abincin da kuke ci, Likita ya shawarci masu ciwon gyambon ciki

- Masu ciwon gyambon ciki soyayyen abinci na iya tayar masu da shi, yayin da wasu kuma tsattsauran abinci i irin garin rogo zai iya tayar masu da ciwon.

- Masu fama da cutar su fahimci irin nau’in abincin dake tayar masu da ciwon gyambon cikin.

Wani kwararren likitan fida dake aiki da assibitin kwararri ta jami’ar Ilori (UITH), Farfesa Ismail Adigun yace mutanen dake fama da ciwon gyambon ciki za su iya yin azumi ta hanyar kauce ma na’ukan abincin dake haddasa masu matsala.

Adigun ya fada ma kamfanin dillancin labarai na Najeriya a cilkin wata zantawa ranar Asabar a garin Ilori, cewa masu fama da cutar su fahimci irin nau’in abincin dake tayar masu da ciwon gyambon cikin.

Yace wasu masu ciwon gyambon ciki soyayyen abinci na iya tayar masu da shi, yayin da wasu kuma tsattsauran abinci i irin garin rogo zai iya tayar masu da ciwon..

Likitan fidar ya shawarci mutane da su rage cin abinci mai zafi, mai yaji da kuma mai sinadarin acid saboda suna kawo matsala ga tsarin narkewar abinci.

Kamar yadda yace, zabi mafi dacewa ga wanda ke fama da cutar gyambon ciki idan zai dauki azumi, shine ya bambanta abincin da yake ci a duk tsawon watan ta hanyar hada shi da dukkan nau’ukan sinadaran gina jiki.

Yayi gargadin a guji soyayyen abinci, abinci mai kitse, lemun tsami, tumaturin gwangwani mai dauke da sinadarin acid, da sauran na’ukan abinci masu tsami.

KU KARANTA: Gwamanatin tarayya na kokarin shawo kan matsalar tsaro — Buhari :

Don haka masu fama da ciwon su yi taka tsan-tsan a lokacin buda baki, a ci abinci ba da yawa ba, amma akai-akai.

“Misali a fara da dabino da abinci maras nauyi sannan a dan huta, daga baya kuma sai a ci abinci.” In ji likitan.

Watan Ramadan shine watan tara a kalandar Musulunci, wanda a cikin shi dole ne ga kowane lafiyayyen baligin Musulmi ya yi azumi a lokacin yini. Musulunci ya dauke ma mutanen da ba su da lafiya daukar azumi.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel