Marigayi Abacha bai yarda da zaman jami'o'in da ba na gwamnati ba: In ji tsohon magatakardar hukumar kula da jami'o'i

Marigayi Abacha bai yarda da zaman jami'o'in da ba na gwamnati ba: In ji tsohon magatakardar hukumar kula da jami'o'i

- Marigayi shugaba Abacha ya bada umurni ba a rubuce ba cikin shekarar 1996 na dakatar da bada izinin buda jami’o’in da ba na gwamnati ba.

- Janar Abubakar ya yabi Chief Igbinedion kan fafutukar nema wa jami’o’in da ba na gwamnati ba lasisi har tsawon shekaru tara ba tare da kasawa ba.

Wani tsohon sakataren zartarwa na hukumar jami’o’i ta kasa Farfesa Munzali Jibril, jiya yace marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha ya tafi da imanin cewa sashe mai zaman kansa na Najeriya bai isa a damka ma shi alhakin mallaka da tafiyar da jami’o’i ba.

Farfesa Jibril yace marigayi shugaba Abacha ya bada umurni ba a rubuce ba cikin shekarar 1996 na dakatar da bada izinin buda jami’o’in da ba na gwamnati ba.

Jibril yayi wannan bayanin ne a lokacin da yake gabatar da wata makala a jami’ar Igbinedion, Okada a bukin cikarta shekaru 20 da kafuwa.

Yace Cif Gabriel Igbinedion, mai rike da sarautar Esaman masarautar Bénin, ya cigaba da fafutukar neman lasisi a lokacin mulkin Abdussalami Abubakar, inda ya roki alfarmar kakkabe kurar fayil din neman bukatar buda jami’i’o’in da ba na gwamnati ba.

KU KARANTA: Gwamanatin tarayya na kokarin shawo kan matsalar tsaro — Buhari

Jibril yace jami’o’in da ba na gwamnati ba da yawa sun nuna halin ko in kula ga bunkasa da walwalar ma’aikatansu saboda suna bada ma’aikata ne kawai don samun yardar gudanar da aiki.

Tsohon magatakardan NUC yayi kira ga jami’o’in da ba na gwamnati ba da su rage yawan kudin makaranta da dalibbai ke biya, saboda ingantattun jami’o’i anan gaba sune wadanda aka kafa ba don neman riba ba.

Janar Abubakar ya yabi Chief Igbinedion kan fafutukar nema wa jami’o’in da ba na gwamnati ba lasisi har tsawon shekaru tara ba tare da kasawa ba.

Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel