Gwamanatin tarayya na kokarin shawo kan matsalar tsaro — Buhari

Gwamanatin tarayya na kokarin shawo kan matsalar tsaro — Buhari

- Yayi kira ga ‘yan Najeriya da su bada ta su gudun mawa don shawo kan matsalar tsaron.

- ‘Yan Najeriya su sa imani a kasarmu mai albarka.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwmanati na iya kokarita na shawo kan matsalolin tsaro dake addabar kasar kanan.

Kuma yayi kira ga ‘yan Najeriya da su bada ta su gudun mawa don shawo kan matsalar tsaron.

Shugaban kasa yayi wannan maganar ne jiya a wani taron da gwamnonin jam’iyyar APC suka shirya, inda suka karrama shi kan jan ragamar jam’iyyar APC da tabbar da ganin ita ce kan gaba a zabubbukan game gari da suka gabata.

KU KARANTA: Wani Lauya ya tafka Buhari kotu kan rashin sanar da majalisar Dokoki da zai tafi

Da yake magana kan kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta a wurin taron, Buhari yace: “Dukan ku kuna sane da cewa matsalar tsaro ta kasance wani babban kalubale gare mu. Muna iya kokarinmu mu fuskanci wannan kalubalen kuma mu mayar da wannan kasar mai cikakken tsaro fiye da shekarun baya.”

“Yayin da tsaron dukiyoyi da rayukkan al’amma yake alhakin gwamnati, haka kuma ya rataya ga wuyan ‘yan kasa da su bada ta su gudun mawa, don samar da tsaro aikin kowane.”

“Ina kira ga ‘yan Najeriya su sa imani a kasarmu mai albarka. Ina godiya gare ku don tabbataccen hankuri da sadaukarwar da kuka yi wurin ciyar da wannan kasa gaba.”

A bangaren tattalin arziki, Buhari yace ta fuskar kalubalen da suka bijiro daga matsalar rashin kula da al’amurran tattalin arzikin kasa da siyasa da aka samu a baya, dole ne jam’iyyar ta yi alfaharin taka rawar gani wurin farfado da darajar Najeriya a cikin shekaru hudu da suka wuce, a fannin bunkasa dan Adam da samar da abubuwan more rayuwa.

Yace: “A tsaye muke don ganin mun inganta rayuwar ‘yan Najerya”

Yayi kira kan bukatar da ake akwai ta gina gadoji a duk fadin kasar nan.

A lokacin da wasu ‘yan tsirarun shafaffin mutane da kungiyoyi suka zabi juya matsalolin addini da kabilanci don neman wata biyan bukata tasu, muna da bukatar gina gadojin da zasu hada al’amurra daban-daban, da kuma kasancewa tsintsiya madaurinki daya a kasa daya,” In ji Buhari.

Shugaban kasa kuma ya bukaci gwamnanin da su taimaka ma yakin da gwamnati take yi da almundahana.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel