Yara mata miliyan 6 ba su cikin makaranta a Najeriya – In ji Fayemi

Yara mata miliyan 6 ba su cikin makaranta a Najeriya – In ji Fayemi

- Miliyoyin manya da yara mata, kamar yadda tace suna fuskantar matsalar talauci, rashin damar samun abubuwan more rayuwa, cututtuka, rikice-rikice da kuma matsalolin al’ada

- Yawan mata masu wakilci a majalisar dokoki ta kasa da wasu bangarorin gwamnati ba abun azo a gani ba ne

Matar gwamnan jihar Ekiti, Mrs Bisi Fayemi, ta koka game da karuwar yawan yara da ba su halartar makaranta a kasar nan, yawan yara mata da ba su halartar makaranta ya kai miliyan shidda daga cikin miliyan 10.5 wadanda ba su da halin shiga makarantun boko a kasar nan.

Mrs. Fayemi ta bayyana cewa yawan mata masu wakilci a majalisar dokoki ta kasa da wasu bangarorin gwamnati ba abun azo a gani ba ne, tare da tabbatar da cewa abubuwa za su kyautu da irin wayar da kan mata da ake yi.

KU KARANTA: Buhari ya tabbatar da nadin sabon shugaban hukumar matasa masu yi wa kasa hidima NYSC

Ta bayyana hakan ranar Larba lokacin da take gabatar da wata lacca mai suna ‘Tafi da Hannu Daya, Ilimin Mata, Shugabanci da Bukatar Bunkasar kasa’ a jami’ar kiyon kimiyyar lafiya dake birnin Ondo a jihar Ondo.

A cikin laccar Mrs Fayemi tace yawan rashin tsaro a yankin arewa maso gabas na kasar nan da yawan kashe-kashe, kuma garkuwa da kananan yara mata a wasu bangarorin Najeriya ya shafi ilimin kananan yara da yawa, wanda tace zai shafi makomar Najeriya.

Miliyoyin manya da yara mata, kamar yadda tace suna fuskantar matsalar talauci, rashin damar samun abubuwan more rayuwa, cututtuka, rikice-rikice da kuma matsalolin al’ada.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel