Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan

Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan

-Wata mata ta sayar da diyar cikinta akan kudi N600,000 kacal

-Matar tace tayi amfani da kudi wajen sayen waya, atamfa da takalmi kuma tana da niyyar yin kasuwanci da ragowar kudin

Rundunar yan sanda reshen jihar Imo ta kama Nneka Donatus yar shekara 27 da haihuwa wacce ta sayar da diyarta bayan ta haifeta da kwana guda.

An damke wannan matar ne tare da wasu mata biyu wadanda ke aiki a ma’aikatar lamuran mata ta jihar, Ujunwa Udechukwu da Nneoma Onwusereaka bisa dalilin taimakon matar wurin sayar da wannan jaririya.

Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan

Abin mamaki: Uwa ta sayar da diyarta kan kudi kalilan
Source: UGC

KU KARANTA:Dalibai sunyi zanga-zanga kan cire shugaban jami’ar Kwara

Mahaifiyar yarinyar wacce ta zanta da yan jarida a shelkwatar yan sandan dake Owerri ranar Alhamis ta amsa laifinta na sayar da diyarta inda tace tayi amfani da kudin wurin sayen wayar hannu, atamfa da kuma takalmi kuma tayi amfani da ragowar kudin domin fara kasuwanci.

Matar ta shaidawa wakilinmu cewa bata iya rike wannan jinjira saboda ta riga da ta haifi diya biyar kafinta.

Matar wacce tayi magana cikin harshen igbo tace: “ Na sayar da diyata N600,000, inda na dauki N15,000 na saya waya, zane da kuma takalmi. Kana kuma duk cikin kudin nah au abin hawa na dawo gida.

“ Na fadawa Nneoma tareda mijinta cewa suyi amfani da ragowar kudin domin fara mani kasuwanci. Ina da diya biyar kuma mun rabu da mijina.” Inji mahaifiyar ‘yar.

Wata mata wacce keda sa hannu cikin lamarin tace itama an bata N10,000 sakamakon kawo mai sayen diyar da tayi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel