Ahmed Aliyu da APC na neman kotun sauraren korefe korefen zabe ta janye damar da ta baiwa Tambuwal
-Ahmed Aliyu na neman kotun korafe-korafen zabe ta hana Tambuwal yin binciken kayayyakin zaben na INEC
-Kotun korafe-korafen zaben ta baiwa Tambuwal damar binciken kayan da akayi zaben gwamanan jihar Sakkwato ranar 9 ga watan Maris, 2019
Dan takarar gwamnan jihar Sakkwato a karkashin jam’iyar APC a zaben gwamnan ranar 9 ga watan Maris, 2019 Alhaji Ahmad Aliyu shine ya shigar da kara akan kotun ta hana Aminu Waziri Tambuwal binciken kayayyakin zaben.
Kotun korafe-korafen zaben a farko ta baiwa Tambuwal damar yin binciken kayayyakin zaben da hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa (INEC) tayi amfani dasu wurin zaben a ranakun 9 ga watan Maris da kuma 23 ga watan Maris da ake sake yin zaben bayan na farko bai kammalu ba.
KU KARANTA:Majalisar zartarwa ta tarayya ta ware N970.2m domin gina barikin hukumar kwastam
A damar da aka baiwa masu wakiltar Tambuwal da jam’iyar PDP akwai yancin binciken hadda kayayyakin sirri na hukar zabe.
Jagogaran lauyoyin dake wakiltar Ahmed Aliyu da jam’iyar APC Jacob Ochidi a zaman da kotun tayi yau Alhamis ya nemi a soke wannan damar da aka baiwa Tambuwal na yin bincken wadannan kayayyaki saboda akwai kayayyakin aiki na sirri a ciki.
Ochidi ya roki kotun ta dage sauraron wannan kara, inda yake cewa basu da halin cigaba da kalubalantar karar saboda karancin lokacin da suka samu kafin zuwa wannan zama.
“ A matsayinmu na masu korafi, muna da niyyar tattara bayanai masu kunshe da hujjoji wanda zamu gabatarwa kotu. Mataki uku wannan abin zai biyo kafin zuwa gaban wannan kotun a ranar da aka bukace shi. A jiya ne kuma muka samu wannan takarda a don haka muna bukatar karin lokaci.” Inji Ochidi.
Da yake karin bayani akan abinda Ochidi yace, Barrister Abdulhamid Zubair cewa yayi “ Muna son a rage daga cikin ababen da aka baiwa Tambuwal damar aiwatarwa saboda sunyi tsauri da yawa kuma sun sabawa kudurin kotun korafe-korafen zabe.” A cewar Abdulhamid.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng