Karfin wutar lantarki ya ragu sanadiyyar matsalar da ta faru sau biyu cikin sa’o’i 18

Karfin wutar lantarki ya ragu sanadiyyar matsalar da ta faru sau biyu cikin sa’o’i 18

- Hakan ya faru ne kasa da sa’o’i 18 bayan irin wannan matsalar ta afku a ranar Larba da rana

- Duk da kasancewar har yanzu ba a gano dalilin faruwar hakan ba, jami’an kamfanin samar da wuta na Najeriya sunce suna aiki tukuru don magance matsalar wutar lantarkin da faru.

Karfin wutar lantarki na kasa ya sake samun matsala ranar Alhamis da karfe 5:30 na safe, kamar yadda wata majiya daga kamfanin samar da hasken wutar lantarki na kasa ya sanar.

Wannan ya faru ne kasa da sa’o’i 18 bayan irin wannan matsalar ta afku a ranar Larba da rana.

Yayinda aka samu shawo kan matsalar ta ranar Larba da marece, sabuwar matsalar ta bar jihohi da dama ba tare da hasken wutar lantarki ba baki daya.

Wata majiyar sirri ta bayyana cewa kusan tsawon sa’o’i biyu, dukkan rukunonin Kamfanin samar dawutar lantarki na Abuja (AEDC) da suka hada da Kogi, Abuja, Nasarawa da Neja suna kan rashin megawatts watau ba su da wutar lantarkin baki daya.

KU KARANTA: Al'ummar Gaya, Rano, Bichi da Karaye sunyi tururuwa zuwa majalisar Kano don nuna farin ciki

Matsalar kuma ta shafi jihohi kamar Sakkwato, Kaduna, Kano da Katsina wadanda ke karkashin kamfanin samar da wuta na Kaduna Electric da Kano DisCo, kamar yadda rahotonni suka bayyana.

Duk da kasancewar har yanzu ba a gano dalilin faruwar hakan ba, jami’an kamfanin samar da wuta na Najeriya sunce suna aiki tukuru don magance matsalar wutar lantarkin da faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewarku tare da mu. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel