Abin al’ajabi: Wani masoyin Liverpool ya mutu bayan kungiyarsa ta doke Barcelona

Abin al’ajabi: Wani masoyin Liverpool ya mutu bayan kungiyarsa ta doke Barcelona

-Wani matashi ya mutu yayin murnar nasarar da kungiyar Liverpool ta samu na fidda Barcelona daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai

-Matashin mai suna Danso Atiko dalibine a makarantar koyar da fasaha da kere-kere ta Akwaita dake kasar Ghana inda yake zana jarabawar karshe kan ya mutu

Wani masoyin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dan asalin kasar Ghana ya rasa rayuwarsa yayinda ya fadi lokacin da Liverpool ta doke Barcelona da 4-0 a wasan zagayen kusa da na karshe na kofin zakarun nahiyar turai.

Wannan mutum mai suna Hebert Danso Atiko, an sameshi ne a kasa shame-shame bai san inda kansa yake ba, bayan murnar cewa kungiyar da yake goyon baya ta Liverpool tayi nasara a wani gidan kallon kwallo dake gabashin kasar Ghana.

Abin al’ajabi: Wani masoyin Liverpool ya mutu bayan kungiyarsa ta doke Barcelona

Abin al’ajabi: Wani masoyin Liverpool ya mutu bayan kungiyarsa ta doke Barcelona
Source: UGC

KU KARANTA:Babban sufeton yan sanda ya bada umarnin janye masu tsaron wasu daidaikun mutane

Mutanen dake tare dashi sunyi kokarin taimakasa amma hakan bai yi wani amfani ba. Anyi gaggawar kai shi asibiti ta Akwaita St. Dominics inda likita yace masu sai dai kuyi hakuri dan uwanku ya riga gidan gaskiya.

Atiko dai kafin rasuwarsa ya kasance yana shekararsa ta karshe ne a makarantar koyar da kere-kere ta Akwaita inda yake karantar kimiyyar fasaha da kere-kere.

Shugaban makarantar da Atiko yake zuwa mai suna Maxwel Owusu-Afriyie ya shaidawa gidan rediyon tauraro daka Accra cewa ana kan binciken yadda lamarin ya auku.

“ Zamuyi bincike domin gano gaskiyar lamarin. Idan har akwai wani abu na rashin dacewa da daliban keyi zamu dau mataki akansa ta hanyar yi masu gargadi, domin idan irin haka ya faru dama muna tara dalibanmu domin jawo hankalinsu.” Inji shugaban makarantar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel