Kwana 3 da fara Ramadan: Shin an haramta wa Musulmi jin kida alhalin yana azumi?

Kwana 3 da fara Ramadan: Shin an haramta wa Musulmi jin kida alhalin yana azumi?

Tsokacin Edita: Duk da gudanar da salloli, yin azumin watan Ramadan tare da gudanar da ayyukan ibada, wasu musulmai a fadin duniya basu da masaniya kan cewa sauraran kida haramun ne a addinin musulunci.

A wannan lakcan Ramadana. Legit.ng ta binciko cewa sauraran kida haramun ne ga musulmai cikin watan Ramadan ko a sauran watanni a cewar sunna (koyarwar) Annabi Muhammad dan Abdallah.

Hakika furuci mafi alkhairi shine littafin Allah (Al-Qur’an) kuma mafi alkhairin shugabanci ita ce shugabancin Annabi aMuhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), kuma al’amuran sharri sun kasance wadanda aka kirkiro, kuma duk kirkire cikin sabbin al’amura tana batarwa kuma kowace bata tana a wuta. Allah tsiratar damu daga azabar jahannama, (Ameeen).

Sauraran kida haramun ne, ko a Ramadan ko a sauran watanni, amman an fi haramtawa a Ramadan, zunubi ne mai girma, saboda azumi ba hani daga cin abinci da shan ruwa bane kawai illa sanya tsoron Allah a zuciya, wannan yana nufin cewa dukkan gabobi su guji aikata ayyukan haramu.

Allah madaukakin sarki yace: “Ya ku wadanda kuka yi imani! An tilasta muku azumi kamar yanda aka tilasta ma wadanda suka gabata, don ku zama masu tsoron Allah” (Al-Baqarah 2:183).

Saheeh Sunnah na annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya nuna karara cewa sauraron kida haramun ne.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun zaben Shugaban kasa ta fara zama akan karar Atiku, Peter Obi ya hallara

Al-Bukhaari ya ruwaito a Mu’allaq cewa manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yace: “Za a samu daga cikin al’umma ta mutanen da za su dauki zina, siliki, naman alade da jin kida a matsayin halal...”

Hadisin ya nuna cewa kayayyakin wakoki haramun ne a fanni biyu:

1. Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace, “Za su dauke shi... a matsayin halal.” Wannan karara ya nuna cewa abubuwan da aka ambata haramun ne, amma mutane za su dauke su a matsayin halal.

2. An ambaci kayayyakin waka tare da abubuwan da aka haramta, kamar zina da shan giya. Idan ba haramun bane da ba a ambace su tare ba (Al-Silsilah al-Saheehah daga al-Albaani, hadisi na 91).

Azumi a Musulunci na tattare da tsarkakewa mafi girma. Babban manufarsa shine horar da mai imani tsarkin zuciya da kuma na sarari. Don haka, domin ganin mun cimma alfanun auzmi, ya zama dole mu guji duk wani mumunan ayyuka ba wai kawai mu hana kanmu cin abinci das ha bane azumi. Azumi na hakika ya hada da kare ganinmu, kunnuwanmu, hannayenmu, kafafuwanmu, da kuma zukatanmu daga aikata laifuka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel