Sabon majalisar Buhari: Yan siyasa 15 na kamun kafa domin samun kujerar minista a wata jihar Kudu

Sabon majalisar Buhari: Yan siyasa 15 na kamun kafa domin samun kujerar minista a wata jihar Kudu

Yayinda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke duba yiwuwar ganin majalisarsa ta kunshi manyan yan Najeriya, akalla mutane 15 a jihar Cross River ne suka nuna soyuwarsu ga wannan mukami, wanda hakan zai sa duk wanda yayi nasarar samun mukamin zama dan jam’iyya mai mulki mai rike da mukami mafi daraja a jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mafi akasarin manyan yan siyasar APC da ke zawarcin wannan kujera sun kasance yan takarar kujerar gwamna, da mukaman majalisar dokoki na kasa da jiha wadanda suka fadi zabe a jihar inda jam’iyyar adawa ta PDP tayi nasara.

Bincike ya kuma bayyana cewa adawa da rabuwar kai a jam’iyyar APC reshen jihar, wanda ya haddasa faduwarsu a zaben kasar da ya gudana, ya girmama yayinda ake kokarin zabar minister daga jihar.

A cewar wata majiya abun dogaro, manyan yan takarar na tunkawo ga kusancinsu ga imam Shugaban kasa Buhari ko kuma shugabancin APC a matakin kasa da yanki kuma basu da niyan janyewa duk da cewar da aka yi Shugaban kasar zai zabi yan majalisarsa akan cancanta ba wai kasancewar mutum dan majalisa ko kuma wanda ya bayar da gudunmawa ba.

Sabon majalisar Buhari: Yan siyasa 15 na kamun kafa domin samun kujerar minista a wata jihar Kudu
Sabon majalisar Buhari: Yan siyasa 15 na kamun kafa domin samun kujerar minista a wata jihar Kudu
Asali: Facebook

Daya daga cikin masu zawarcin mukamin, wanda aka ce ya fara tattaunawa don shiryawa da wadanda ya bata mawa a yayin zaben da ya gudana a jihar, ya kasance mamba a majalisar dokokin kasa, yayinda wani kuma dan takarar mukamin ya kasance makusancin Buhari.

Sai dai yayinda ake ci gaba da tseren, manyan mambobin jam’iyyar, wadanda suka fusata da faduwarsu zabe a jihar da kuma kujerun majalisar dokoki, sun fara yunkurin hana duk yan siyasar da suka haddasa hakan samun kowani mukami.

KU KARANTA KUMA: Buhari da APC ne ya kamata su dauki alhakin rashin tsaro – Atiku

A cewar majiyoyi, shugabannin jam’iyyar sun nusar da Shugaban kasar, inda suka tunasar dashi kan yaudarar da wadanda ke neman mukamin suka yi ma jam’iyyar.

Wani jigon APC a jihar Cross River kuma mataimakin ma’ajin kungiyar kamfen din Shugaban kasa, Cif Utum Eteng yayinda yake martani ga lamarin, ya gargadi Shugaban kasa da kada ya ba kowani dan siyasa da ya haddasa faduwar jam’iyyarsa mukamin minista.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel