Mu na iyaka bakin kokari wajen inganta tsaro a Najeriya - Babban Sufeton 'Yan sanda

Mu na iyaka bakin kokari wajen inganta tsaro a Najeriya - Babban Sufeton 'Yan sanda

Sufeto Janar na 'yan sandan Muhammad Adamu, a ranar Talata ya shaidawa 'yan majalisar tarayya yadda hukumar sa ta tsaro ke iyaka bakin kokarin ta wajen kawo karshen kalubale na rashin tsaro da ya zamto annoba a kasar nan tare da kasancewa katutu a gare ta.

Yayin amsa goron gayyata, babban sufeton na 'yan sanda ya bayyana a zauren majalisar dattawa domin yi ma ta karin haske musamman a kan yadda masu ta'ada ta cin kasuwar garkuwa da mutane ke yadda su ke so a kasar nan.

Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya; Muhammadu Adamu
Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya; Muhammadu Adamu
Asali: Twitter

Rahotanni kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaitosun bayyana cewa, babban jagoran na hukumar 'yan sanda ya bayyana a zauren na Sanatoci tare da mai bayar da shawara ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan harkokin da suka shafi majalisar tarayya, Ita Enang.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar dattawan Najeriya ta aike da sakon gayyata na neman sufeton 'yan sanda ya bayyana a gaban ta tun a ranar 25 ga watan Afrilun 2019 domin jin ta bakin sa dangane da daurin damarar sa na warware barazanar rashin tsaro a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Kalubalantar sakamakon zabe: Za a fara sauraron karar Atiku a ranar Laraba

Majalisar ta yanke shawarar neman jin ta bakin sufeton 'yan sanda biyo bayan wani kudiri da wakilin shiyyar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya gabatar musamman yadda masu ta'adar garkuwa da mutane suka addabi matafiya a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, mun samu cewa kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, ta kai wani mummunan farmaki yankin Molai daura da birnin Maiduguri na jihar Borno.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel