Harin kwalejin Filato: An sako yar uwar mataimakin rajistaran kwalejin da aka sace

Harin kwalejin Filato: An sako yar uwar mataimakin rajistaran kwalejin da aka sace

-Abigail Amos ta kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan da aka biya kudin fansa

-Mataimakin rajistaran kwalejin wanda yake yaya a gareta ya tabbar da gaskiyar wannan zance

Kanwar mataimakin rajistaran Kwalejin fasaha da kere-kere ta Filato mai suna Abigail Amos ta kubuta daga hannun wadanda suka saceta a ranar Litinin.

Abigail wacce ke shekarar farko a matakin diploma a kwalejin ta shiga hannun masu garkuwa da mutane ne yayinda suka kawo wani farmaki a sashen gidajen ma’aikatan kwalejin dake unguwar Heipang dake Barikin Ladi da misalin karfe 12:10 na dare.

Harin kwalejin Filato: An sako yar uwar mataimakin rajistaran kwalejin da aka sace
Harin kwalejin Filato: An sako yar uwar mataimakin rajistaran kwalejin da aka sace
Source: Twitter

KU KARANTA:Ana ci gaba da ragargazar Buhari kan furucin da yayi game da tsaro

Ta kasance tana bacci tare da sauran iyalan gidan mataimakin rajistaran a lokacin da wannan abu ya faro.

Rahotanni sun nuna cewa an sako wannan dalibar ne bayan an biya kudin fansa a daren Litinin kuma aka daukota daidai Kwalejin yan sanda dake Jos inda masu garkuwar suka ajiye ta.

Mataimakin rajistaran, Ezekiel Rangs ya tabbatar da wannan labari a garin Jos ranar Talata.

Rangs yace: “ Hakika mun samu cetota. Ni da kaina na daukota kusa da Kwalejin yan sanda ta Jos da misalin karfe 7:30 na maraice.

“ Mun biya kudin fansa kafin su amince da sakota, amma ba zan so fadin ko nawa bane saboda ina kokarin mantawa ne faruwar wannan lamari.

“ Ta kuma shaida mana cewa ba’a doketa ko kuma cimata zarafi ba yayinda take tsare karkashin masu garkuwar. Mun godema Allah da basu kasheta ba kuma a yanzu ta dawo mana lafiya kalau.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel