Yan hisbah zasu kama duk wanda yaci abinci a fili cikin watan Ramadan

Yan hisbah zasu kama duk wanda yaci abinci a fili cikin watan Ramadan

-Duk wanda yaci abinci gaban jama'a cikin watan Ramadan zamu kama shi, zance daga bakin kwamandan hisbah na Kano

-Ya zama wajibi kowane musulmi ya mutunta watan Ramadan ko yana azumi ko baiyi, inji Nabahani Usman

Babban kwamandan hisbah na Kano, Nabahani Usman yace daga ranar Litinin wacce ake sa ran itace ranar da za’a tashi da azumi jami’ansa zasu fara damke ko wane baligi da aka gani yana cin abinci a fili.

Usman yace duk wanda aka kama ba za’a sake shi ba har sai ya nuna takardar asibiti daga wurin likita cewa yana ciwon olsa wanda ya hana shi yin azumi.

Yan hisbah zasu kama duk wanda yaci abinci a fili cikin watan Ramadan

Yan hisbah zasu kama duk wanda yaci abinci a fili cikin watan Ramadan
Source: Twitter

KU KARANTA:Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu

Kwamandan hisban ya shaidawa BBC cewa idan mutum ya bada takardar shaida ta asibiti zasu sake shi tareda gargadin cewa kada ya sake cin abinci a baina jama’a.

Jagoran hisban cikin kwanakin nan ya kama mutane da yawa da suke aikin karuwanci da kuma wasu ayyukan ashsha iri daban daban saboda zuwan wata mai tsarki na Ramadan.

Ya kara da cewa Ramadan watane na musamman ga musulmi a don haka ya zama wajibi ga kowane musulmi ya azumci wannan wata.

Bugu da kari, “ Duk shekara munayi haka don haka bana ma baza mu fasa ba. Manufar yin hakan kuwa shine domin ya kasance ko wane musulmi ya mutunta watan Ramadan. Ko da likita yace maka kada kayi azumi ai bai kamata ka fito fili kana cin abinci ganin cewa jama’a na azumi.” Ya sake jaddadawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel