Ga bikin zuwa: Gwamnan jihar Kano zai aurar da zawarawa 1500

Ga bikin zuwa: Gwamnan jihar Kano zai aurar da zawarawa 1500

- Gwamnatin Jihar Kano ta shirya aurar da zawarawa guda 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar

- An shirya gudanar da wannan aure ne a yau Asabar, 4 ga watan Mayu inda za a ashe miliyoyin naira daga asusun gwamnati

- Haka zalika gwamnati ce za ta sai wa amaren gado, katifa, da sauran kayan dakin amare da suka hada har da kujeru na kushin

A yau Asabar, 4 ga watan Mayu ne Gwamnatin Jihar Kano ta shirya aurar da zawarawa guda 1,500 a fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar.

A wata sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na gwamna, Abba Anwar ya fitar, ya nuna cewa a yau Asabar ne za a daura aure a dukkan fadin kananan hukumomin jihar.

Anwar ya ce gwamnatin Kano ce za ta biya kudin sadakin kowace naira 20,000 a lokacin daurin auren.

Ya ce za a biya kudin ‘lakadan’ ba ‘ajalan’ ba.

Ga bikin zuwa: Gwamnan jihar Kano zai aurar da zawarawa 1500

Ga bikin zuwa: Gwamnan jihar Kano zai aurar da zawarawa 1500
Source: Depositphotos

An tattaro cewa za a kashe kudi har naira miliyan 30 a wannan aure, kamar yadda yake a sanarwar.

Haka zalika gwamnati ce za ta sai wa amaren gado, katifa, da sauran kayan dakin amare da suka hada har da kujeru na kushin. Su kuma an guna an shirya raba musu shaddar da za su yi ankon biki a ranar daurin auren na su.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa inna illahi raji’un: Jarumar kannywood Binta Kofar Soro ta rasu

Gwamnatin Jihar Kano ta dade ta na shirya wannan al’ada ta aurad da zawarawa da nufin rage yawaitar zawarawa a fadin jihar. Wannan ya samo asali ne tun zamanin mulkin tsohon gwamna Rabi’u Kwankwaso da Ibrahim Shekarau.

An rika shirya auren a karkashin Hukumar Hisba ta Jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel