Wasu ma’aikatan kamfanin lantarki sun shiga hannun hukuma

Wasu ma’aikatan kamfanin lantarki sun shiga hannun hukuma

-Jami'an tsaro sun damke wasu mutum uku ma'aikatan kamfanin bayar da lantarki a Inugu

-Su dai wadannan mutanen ana zarginsu ne da satar mita wacce ake sawa kati mallakar kamfanin bayar da wutan

An kama ma’aikatan kamfanin bayar da lantarki na Inugu su 3 saboda zarginsu da satar mita wacce ake sanyawa kati.

Da take duba mutanen da aka kama, babbar kwamandan jami’an tsaro na farin kaya wato (NSCDC) Chinwe Kannu tace jami’anta sun damke mutanen ne a wurin da kamfanin lantarkin ke gyare-gyare.

Wasu ma’aikatan kamfanin bayar da lantarki sun shiga hannun hukuma

Wasu ma’aikatan kamfanin bayar da lantarki sun shiga hannun hukuma
Source: UGC

KU KARANTA:An shawarci zababben gwamnan Kwara da ya kasance tamkar Ahmadu Bello Sardauna

Sunayen wadanda aka kama sune, Godswill Nnanna, Odianya Chukwudi da Friday Nnanna. Kwamandar ta sake cewa wadannan mutane sun kasance tsofaffin ma’aikatan kamfanin samar da wutar lantarki ne tas kasa wanda aka fi sani na NEPA.

“ Mun kama wadannan mutanen ne a wurin da ake gyare-gyare na kamfanin bayar da lantarki na Inugu wato EEDC wanda ke shiyyar Independence layout.”

“ Wani daga cikin ma’aikatan kamfanin ne ya zo wajen domin daukar mitoci cikin babbar mota guda, tsayawarsa ke da wuya sai ga wasu nan sun fito da kwali dauke da mitoci guda biyu da kuma wasu abubuwa na daban.

“ Jami’inmu dake wannan wuri ya nemi ya san daga ina wannan kwali ya fito, kasancewar ranar babu aiki. Daidai lokacin da ake tuhumar wannan mutum sai ga kira a wayarsa ta salula wanda muke kyuatata zaton cewa kiran wanda suka shirya zai kaima kayan satan ne.” Inji Chinwe.

A karshe ta kara da cewa wadanda ake tuhumar za’a turasu zuwa kotu nan bada jimawa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel