Magu ya yi gaskiya, wasu gwamnoni na satar kudade da sunan magance tsaro - Bafarawa

Magu ya yi gaskiya, wasu gwamnoni na satar kudade da sunan magance tsaro - Bafarawa

- Attahiru Bafarawa ya yarda da furucin Shugaban EFCC Magu na cewa gwamnonin jiha na amfana daga yawan rashin tsaro a fadin kasar

- Magu ya zargi gwamnoni da rura wutar rashin tsaro domin samun rara daga lamarin tsaro a jihohinsu

- Tsohon wamnan na Sokoto yace gwamnonin jiha na kara cika aljihunsu da kudaden da aka ware don tsaronsu

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, kuma tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya yarda da zargin da Shugaban hukumar yaki da ccin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, ya yi na cewa wasu gwamnonin jihohi na fakewa da karya ko gaskiyar matsalar tsaro su na sace makudan kudaden jama’a.

Bafarawa ya jaddada zargin da Magu ya yi a ranar Alhamis, lokacin da ya gudanar da taron manema labarai a kan shirye-shiryen gudanar da Taron Makomar Tsaro A Najeriya, wanda Gidauniyar Attahiru Bafarawa Foundation za ta shirya.

Tsohon gwamnan ya yi magana da Hausa, wajen amsa tambayar, ya ce tabbas Magu ya yi gaskiya, kuma ya na goyon bayan sa.

Magu ya yi gaskiya, wasu gwamnoni na satar kudade da sunan magance tsaro - Bafarawa
Magu ya yi gaskiya, wasu gwamnoni na satar kudade da sunan magance tsaro - Bafarawa
Asali: Twitter

Don haka Bafarawa ya ce gwamnoni a yanzu su rika tafiya suna waiwayen bayan su, su ga gwamnonin da aka yi a baya yaya suka kare.

Bafarawa ya ce taron da Gidauniyar Attahiru Bafarawa Foundation za ta shirya bayan azumi a Kaduna, za a tattauna neman mafitar matsalar tsaron da ta dabaibaye kasar nan ce, da nufin samo mafita.

Ya nesanta taron da siyasa, yayin da ya kara da cewa kuskure ne masu adawa su rika murna idan kasa ta shiga mamuyacin halin da kowa ke ji a jikin sa.

KU KARANTA KUMA: Zamfara: Masu garkuwa sun karbi kudin fansa N2.5m sannan suka sace dan mutumin da suka yi garkuwa dashi

Daga nan ya koka a kan matsalar rashin aikin yi, talauci, rashin ilmi da sauran matsalolin da ake ganin sun haddasa tabarbarewar tsaro, musamman a Arewa.

Duk da haka, Bafarawa ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya kasa cimma wasu nasarori ne, saboda bai samu wadanda za su ba shi maganin da za a sha a warke cutar da ke addabar mu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel