Rikice-rikice: Wata kungiyar matasa ta nuna damuwarta bisa abubuwan dake faruwa a jihar Taraba

Rikice-rikice: Wata kungiyar matasa ta nuna damuwarta bisa abubuwan dake faruwa a jihar Taraba

-Matasan karamar hukumar Takum sun koka dangane da halin da jiharsu ke ciki

-Rokon matasan shine gwamnati ta shiga cikin wannan lamarin domin ayi abinda ya dace

Wata kungiyar matasa dake karamar hukumar Takum a jihar Taraba ta nuna damuwarta dangane da barazanar rashin tsaro da suke fama dashi a yankin.

A wani zance wanda ya fito daga wurin shugaban kungiyar, Irdomiya A. Danjuma yace barazanar rashin tsaron ta sanya mutane da dama sunyi hijira sun bar wuraren zamansu na asali wanda kuma haka zai shafi durkushewar tattalin arziki.

Rikice-rikice: Wata kungiyar matasa ta nuna damuwarta bisa abubuwan dake faruwa a jihar Taraba
Rikice-rikice: Wata kungiyar matasa ta nuna damuwarta bisa abubuwan dake faruwa a jihar Taraba
Asali: Twitter

KU KARANTA:N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

Zance ya kara da cewa, mazauna wannan yankin basu da kwanciyar hankali saboda a koda yaushe suna cikin fargaba , duk al’amuransu na tsayawane da zarar karfe 7 na yamma tayi. Wadanda kuwa ban yan garin ba suna tsoron shigowa.

“ Al’amuran tsaron Takum sun canza daga yadda suke a da, a halin yanzu abin yayi muni kwarai da gaske. Takum garin Janar T.Y Danjuma mai ritaya ne da kuma gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku sai dai har yanzu babu wani mataki da aka dauka.” Irdomiya ya ce.

Kungiyar ta lura cewa an kashe mutane da dama a wannan dan tsakani, inda ciki hadda kashe wani dan majilisar dokokin jihar mai suna Hosea Ibi wanda ke wakiltar gundumar Takum ta 1 a watan Disemban 2017.

“Ranar 1 ga watan Mayu yan sanda sun kama wata mota kirar Toyota Hilux wacce ake zaton ta shugaban karamar hukumar Takum ce, Shiban Tikari. Motar dai tana dauke ne da gawarwaki 2 wadanda ake kokari jefarwa hanyar Kwambai daidai wurin da aka tsinci gawar Hosea Ibi.

Mutum 2 da aka samu cikin motar sune, Nuvalga Bokunga wanda dayane daga cikin direbobin shugaban karamar hukumar da kuma wani Ishaku Williams. A halin yanzu dai gawarwakin da motar na karkashin kulawar yan sanda yayinda ake cigaba da bincike.” Inji Irdomiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel