Wani makiyayi ya shiga gidan kaso saboda aikata kisan kai

Wani makiyayi ya shiga gidan kaso saboda aikata kisan kai

-Laifin kisa ya tura wani mutum zuwa gidan kaso

-Kotun majistiri ta aika da wani makiyayi zuwa gidan yari a dalilin kisan kai

Wata kotun majistiri dake Illorin ta tura da wani makiyayi mai suna, Suleiman Adamu gidan kaso saboda laifin kisan kai da ya aikata.

Mai yanke hukunci a wannan kotun ta majistiri mai suna Maryam Yahaya bata saurari korafin wannan mutum ba, nan take ta aika shi zuwa gidan kaso inda za’a tsare shi na dan lokaci.

Wani makiyayi ya shiga gidan kaso saboda aikata kisan kai

Wani makiyayi ya shiga gidan kaso saboda aikata kisan kai
Source: Depositphotos

KU KARANTA:N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ba zai yiwa ma’aikata komi ba

Haka kuma, ta umarci yan sanda da su kai shi sashen sauraren kararraki dake Kwara domin cigaba da tuhumarsa.

Malama Maryam ta dage sauraron wannan karar zuwa 24 ga watan Mayu. Wanda ya shigar da karar, Abegunde Elijah ya shaidawa kotun cewa shi dai wannan mutum an kama shine ta hanyar amfani da bayanai da aka samu daga wurin dan uwan wanda aka kashe, Mustapha Abubakar.

Elijah yace a daidai lokacinda muke binciken gidan wanda ya aikata laifin mu samu bindigogi kala daban daban, albarusai da kuma takalman roba kafa biyu.

Ya kara da cewa bincikenmu ya tabbatar mana cewa wanda ake zargin shi ya kashe Abdulkareem Musa a gidanshi dake karamar hukumar Moro a jihar Kwara.

Mai shigar da karar yace wannan laifin yaci karo da sashe na 221 daga cikin dokokin Penal code.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel