Hukumar FAAN ta rufe tashoshin jirgin sama na Gombe da Kebbi kan bashin N732m

Hukumar FAAN ta rufe tashoshin jirgin sama na Gombe da Kebbi kan bashin N732m

Hukumar tashoshin jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta janye jami’anta da ke samar da tsaro daga hatsarruka da kashe gobara daga tashoshin jiragen sama na Gombe da Kebbi akan bashin fiya da naira miliyan 732 da ake bin su.

Babban Manajan harkokin hukumar FAAN, Misis HenrietteYakubu, ta tabbatar da lamarin ga kamfanin Dillancin Labarai (NAN) a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu a Legas.

Yakubu tace janye ayyukan FAAN daga tashoshin jiragen saman, wanda yayi sanadiyar tsayar da ayyukan tashin jiragen sama ya fara ne daga ranar 1ga watan Mayu.

Hukumar FAAN ta rufe tashoshin jirgin sama na Gombe da Kebbi kan bashin N732m

Hukumar FAAN ta rufe tashoshin jirgin sama na Gombe da Kebbi kan bashin N732m
Source: UGC

A cewar FAAN, tashar jirgin Gombe, wanda ke karkashin gwamnatin jihar Gombe, ta kasance da bashin hukuman kimanin naira miliyan 607.9, yayin da tashar jihar Kebbi tana da bashin FAAN naira miliyan 124.5.

FAAN, a wani sanarwa ga matukan jirgi (NOTAM), a baya a watan Afrilu tayi barazanar janye ayyukanta daga tashoshin jirgin saman da sauran tashoshi wadanda hukumar ke bin bashi sannan ta bada wa’adin ranar 30 ga watan Afrilu don biyan basussukan su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

Hukuman ta bayyana cewa baza ta cigaba da ajiye jami’anta a tashoshin jirgin saman ba, ba tare da ta biya ma’aikatan ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel