Abinda yakamata mutum yayi idan ATM yaki biyanshi kudi

Abinda yakamata mutum yayi idan ATM yaki biyanshi kudi

-Matsalar ATM na da matukar cin rai amma kuma idan ta faru ana iya shawo kanta

-Abu mafi kyawo shine mutum yayi saurin sanar da bankinsa matsalar idan har ta faru dashi

Abune wanda kan dau tsawon lokaci kafin ya faru amma sai dai wani lokacin idan mutane sukayi amfani da ATM su kan samu matsalar rashin fitar kudi duk da cewa zaka samu sako daga bankinka cewa ka fitar da kudin.

Wasu lokutan matsalace ke sa ATM din ya hanaka kudi, a wani lokacin kuma idan abin ya shafi yaudarar yan damfarane hakan ke faruwa. Duk da cewa ana mangance irin wannan matsaloli a ko da yaushe sai dai kuma akwai kosawa da mutum kan iya yi kafin a warware matsalar.

Abinda yakamata mutum yayi idan ATM yaki biyanshi kudi

Abinda yakamata mutum yayi idan ATM yaki biyanshi kudi
Source: UGC

KU KARANTA:Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

Wace hanya za’abi domin magance matsalolin ATM?

A wasu lokuta bankin naka zasu san da matsalar kuma su gyara maka ba tare da ka kirasu a waya ba. Wani lokacin kuwa abun ya kan sha ban-ban. A don haka abu mafi da cewa shine idan ka samu matsalar rashin fitar kudi daga ATM kayi gaggawar sanar da bankinka.

Haka zalika, idan hart a kama zaka iya daukan bayanin ATM din da kayi amfani dashi a matsayin shaida. Ana iya daukar hoton ATM din ma don akasarin bankuna suna sanya jerin ATM ne a wuri guda.

Harwa yau akwai bukatar shi mai amfani da katin ya tabbatar cewa ATM din ya sanya kati nasa yayi daidai da irin katin. Idan aka samu sabani hakan zai iya haifar da matsala. Tarin duk wadannan bayanai ne zai baiwa banki damar wareware bakin zaren wannan matsala.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel