An sace Shanu fiye da 300 a jihar Filato

An sace Shanu fiye da 300 a jihar Filato

A yayin da aka nemi mutum guda aka rasa baya ga salwantar rai guda, an sace shanu fiye da 300 tare da sheke su a kauyukan Kuru, Maiyagan da kuma Rekwechungu da kananan hukumomin Jos ta Kudu da Bassa a jihar Filato.

An sace Shanu fiye da 300 a jihar Filato

An sace Shanu fiye da 300 a jihar Filato
Source: UGC

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da kuma kungiyar Matasan Fulani ta Jonde Jam, sun yi zargin cewa tsagerun Irigwe da ke yankin Miyango ke da alhakn zartar da wannan mummunan hari kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jagoran kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato, Muhammad Nuru Abdullahi, ya ce an tsinto gawawwakin shanu 29 a kauyen Kuru, yayin da kidaya a gaban hukumomin tsaro ta tabbatar da adadin shanu 314 da aka tsinto gawawwakin su daura da makarantar nazarin tattali da ke gundumar Kwal a karamar hukumar Bassa.

Abdullahi ya bayyana cewa harin ya salwantar da rayuwar wani matashi Shehu Sa'idu yayin da a halin yanzu an nemi wani matashin Mubarak Adamu an rasa.

KARANTA KUMA: Ruftawar gini ta raunata Mutane 8 a garin Ibadan

Rahotanni sun bayyana cewa, mamallakan shanu sun hadar da Dauda Jalo, Inusa Jalo, Muhammad Adamu, Sani Alhassan, Abdulkadir Sa'idu, Kabiru Muhammad, Yakubu Mahmud da kuma Auwal Abubakar.

Kwamandan rudunar dakarun soji mai fafutikar tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato, Manjo Janar Augustin Agundu, ya yi Allah wadai da aukuwar wannan mummunar ta'ada da ya misalta a matsayin hassada gami da zalunci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel