Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen

Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen

Hankalin yan siyasan Najeriya da jam’iyyunsu na a tashe yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi yunkurin tabbatar da dokar zabe na 2010 akan kashe kudin kamfen.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar INEC ta samu rahotanni daga ofishohinta na jiha kan yan siyasa da jam’iyyun siyasa da suka keta doka a lokacin yakin neman zabensu na 2019.

An dai gudanar da zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokokin kasa a ranar 23 ga watan Fabrairu yayinda aka gudanar da na gwamnoni da na yan majalisun jiha a ranar 9 ga watan Maris a fadin kasar.

Majiyoyin INEC abun dogaro sun bayyana cewa hukumar ta fara harhada jerin masu laifi daga ofishoshinta na jiha 10 wanda zuwa yanzu sun rigada sun gabatar da rahotanninsu kan saba ka’idar kashe kudin kamfen din.

Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen
Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen
Asali: UGC

Kafin gudanar zabeen 2019, INEC ta bayar da iya kudin da ake so yan takarar kujerar Shugaban kasa za su kashe wanda ya kai kimanin naira biliyan daya yayinda yan takarar gwamna kuma aka nemi su kashe naira miliyan 200.

Sanatoci da yan takarar kujerar majalisar wakilai, hukumar ta sa kudin da za su iya kashewa kan naira miliyan 40 da kuma miliyan 20, kamar yadda sashi na 91 na dokar zaben 2010 ta tanadar.

A wajen da wani ya karya doka, a zaben Shugaban kasa zai biya tarar baira miliyan daya ko kuma shekara daya a gidan yari koma dukka biyun.

Ga yan takarar gwamna, wanda aka kama da laifi zai biya tarar N800,000 ko watanni tara a gidan yari ko dukka biyun, yayinda yan takarar sanata za su biya tarar N600,000 ko watanni shida a gidan yari ko dukka biyun.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi

Ga mambobin majalisar wakilai, wanda ya taka doka, zai biya tarar N500,000 ko watanni biyar a gidan yari ko dukka biyun, yayinda yan majalisun jiha da suka karya doka za su biya tarar N300,000 ko watanni uku a gidan yari ko dukka biyun.

An tattaro cewa ofishoshin INEC na jiha sun gabatar da rahotanninsu ga hedkwatar hukumar sannan sun jera sunayen yan siyasar da suka wuce adadin kudin da ya kamata su kashe a lokacin kamfen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel