Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

- Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta shirya wani taro na musamman domin sabbi da gwamnoni masu dawowa

- An shirya taron ne domin marawa gwamnoni masu zuwa baya wajen ci gaban muhimman ayyuka wanda zai basu damar isar da shugabanci nagari

- A ranar 29 ga watan Mayu ne dai za a rantsar da zababbun gwamnonin

Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta shirya wani taro na musamman domin sabbi da gwamnoni masu dawowa gabannin bikin rantsar dasu a ranar 29 ga watan Mayu a Transcorp Hilton, Abuja.

Manufar taron shine domin marawa gwamnoni masu zuwa baya wajen ci gaban muhimman ayyuka wanda zai basu damar isar da shugabanci nagari.

Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

Gwamna Ganduje, El-Rufai, Badaru da kuma zababben gwanmnan Imo Emeka Ihedioha
Source: Twitter

Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo da Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Yari a wajen taron
Source: UGC

Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

Manufar taron shine domin marawa gwamnoni masu zuwa baya wajen ci gaban muhimman ayyuka wanda zai basu damar isar da shugabanci nagari
Source: Twitter

Kayatattun hotuna yayinda kungiyar NGF ta shirya wa zababbun gwamnoni liyafa

Gwamna Yahaya Bello na Kogi da takwarorinsa a wajen liyafar
Source: Twitter

Da farko, Legit.ng ta rahoto cewa sakataren kungiyar gwamnonin Najeriya yace sun kamala shirye-shirye domin gudanar da taron wayar da kai ga zababbu da gwamnoni masu dawowa.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari

A wata sanarwa daga Abdulrazaque Bello-Barkindo, jagoran, harkokin labarai da jama’ a na kungiyar, yace za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun 28 ga watan Afrilu da 2 ga watan Mayu.

Bello-Barkindo yace an shirya taron ne don tallafa wa gwamnoni masu zuwa wajen ci gaban muhimman ayyuka wanda zai basu damar isar da shugabanci nagari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel