Yanzu Yanzu: Yawan mutanen Najeriya ya tasar ma miliyan 201

Yanzu Yanzu: Yawan mutanen Najeriya ya tasar ma miliyan 201

Hukumar kula da asusun yawan jama’a na majalisar dinkin duniya (UNFPA) tace yawan yan Najeriya ya tasar ma miliyan 201 a yanzu.

A rahotonta na yawan mutanen duniya na 2019, UNFPA tace yawan yan Najeriya na a tsaka-tsaki na kaso 2.6 cikin dari daga 2010 zuwa 2019.

Yawan haihuwa a tsakanin matan Najeriya ya sauka daga 6.4 a 1969 zuwa 5.3 a 2019; hakan na nufin matan Najeriya na haifan akalla mutane biyar.

Yawan haihuwa a duniya a kan kowace mace na a 4.8 a 1969; 2.9 a 1994; da kuma 2.5 a 2019.

Yanzu Yanzu: Yawan mutanen Najeriya ya tasar ma miliyan 201
Yanzu Yanzu: Yawan mutanen Najeriya ya tasar ma miliyan 201
Asali: Depositphotos

Rahoton yace yawan mata masu shan maganin hana haihuwa a Najeriya tsakanin shekaru 15-49 kaso 19 cikin dari ne kacal.

Hakan na nuni ga cewa kaso 49 na matan Najeriya na da ikon yanke hukunci akan lafiyar haihuwarsu da yancinsu.

KU KARANTA KUMA: Ganda mai guba ya shiga kasuwar Lagas – Gwamnati tayi gargadi

Hukumar majalisar dinkin duniyan tayi kiyasin cewa yawan yan Najeriya ya karu daga miliyan 54.7 a 1969 zuwa miliyan 105.4 a 1994 da kuma miliyan 201.0 a 2019.

Daga cikin miliyan 201 dinnan, kaso 44 ko miliyan 88.44 na tsakanin shekaru 0 da 14, yayinda kaso 32, 64.32 ke a tsakanin shekaru 10 da 24.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel