Ganda mai guba ya shiga kasuwar Lagas – Gwamnati tayi gargadi

Ganda mai guba ya shiga kasuwar Lagas – Gwamnati tayi gargadi

- An ja kunnen mazauna jihar Lagas kan barazanar da fatar shanu wato ganda ke dashi ga lafiyarsu

- Kwamishinan lafiya na jihar Lagas, Jide Idris, yace gwamnatin jihar ta kama mutum uku da ke da nasaba da siyar da ganda mai guba

- An kama mutanen ne a yankin kananan hukumomin Ojo da Iba

An gargadi mazauna jihar Lagas kan barazanar da fatar shanu wato ganda ke dashi ga lafiyarsu.

Kwamishinan lafiya na jihar Lagas, Jide Idris, yace gwamnatin jihar ta kama mutum uku da ke da nasaba da siyar da ganda mai guba a Ojo da kuma Iba.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Adeola Salako, daraktan harkokin jama’a na jihar Lagas yace an samu ganda mai guba da yawa daga hannun wadanda aka kama.

Ganda mai guba ya shiga kasuwar Lagas – Gwamnati tayi gargadi

Ganda mai guba ya shiga kasuwar Lagas – Gwamnati tayi gargadi
Source: UGC

“Kwamishinan lafiya, Dr. Jide Idris, wanda ya bayyana hakan a ofishinsa a ranar Lahadi yayinda yake duba rahoton kwamitin bincike da aka kafa kan ganda mai guba a yankunan, ya bayyana cewa an tura mutaneuku da ke da hannu a lamarin zuwa kotu, yayinda aka tura samfarin gandar zuwa dakin bincike na NAFDAC domin gwajin ko yana da kyau ga lafiyar dan Adam,” inji Salako.

Jawabin yace masu siyar da gandar na aiki a lokuta mabanbanta a wurare daban-daban a kananan hukumomin Ojo da Iba da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Sai na kawo karshen ta’addanci a Najeriya – Shugaban yan sanda ya dau alkawari

A halin da ake ciki, a baya Legit.ng ta rahoto cewa waata daliba mace daga makarantar poli na jihar Lagas (LASPOTECH) ta mutu bayan ta sha maganin bera.

An rahoto cewa ta aiwatar da mumunan aikin ne a gidan iyayenta, sai dai har yanzu ba a san dalilinta na kashe kanta ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel