Wata mata ta farfado daga doguwar suma ta tsawon shekara 27

Wata mata ta farfado daga doguwar suma ta tsawon shekara 27

Wata mata yar kasar UAE ta farfado bayan wata doguwar suma da tayi a shekara ta 1991.

Munira Abdulla ta samu mummuna rauni a kwakwalwarta bayan wata hatsarin mota data yi shekaru 28 da suka wuce a birnin Al Ain.

A lokacin tana da kimanin shekara 32, ta rungume danta domin cetonsa a yayinda wata motar makaranta ta hadu da motarsu

Bayan shekara hudu babu alamar samun sauki amma ta fara nuna alamar warkewa a shekarar data gabata bayan kula da ta samu a kasar Jamus.

Danta, Omar Webair, Ya bayyana ma Yan jarida cewa ”Ban taba cire tsammani gareta ba dan nasan wata rana zata tashi.”

“Mahaifiyata tana zaune dani a kujerar baya. A lokacin data ga mota zata shigo mana sai ta rugume ni domin ta kare ni.”

Omar ya samu rauni kadan amma mahaifiyarsa ta samu mummunan rauni a kwakwalwarta wanda aka dauki tsawon awanni ba’a mata magani ba.

Daga baya sai aka kaita asibiti, Sannnan aka mata transfa zuwa London domin magani.

KU KARANTA: Yadda na koyawa Sanata Kwankwaso siyasa a kasar nan

An kai Munira kasar UAE, Inda aka dauki tsawon shekaru ana bata abinci ta roba da kuma motsa jiki saboda kar tsokar jikinta ta hade.

A shekara ta 2017, Gwamnatin Abu Dhabi ta kawo dauki ga iyalinta domin akai ta kasar Jamus dan magani.

Bayan shekara daya sai ta fara wasu irin maganganu, Bayan kwana 3 kuma ta ambaci sunan danta Omar.

Omar yace “Nayi mafarkin wannan rana, gashi sunana ne ta fara kira nayi farincikin kasancewar hakan."

Yanzu an dawo da ita kasar Abu Dhabi, Wurin iyalinta inda za’a cigaba da yi mata magani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel