Hotuna: Ayyuka 4 da shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar yau a jihar Legas

Hotuna: Ayyuka 4 da shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar yau a jihar Legas

Sakamakon ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa jahar Legas a yau Laraba, 24 ga watan Afrilu, gwamnatin jahar Legas ta sanar da rufe wasu hanyoyi guda bakwai domin baiwa shugaban damar tafiye tafiye a garin ba tare da wata matsala ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikatar watsa labaru ta jahar Legas ta bayyana cewa ziyarar ta shugaba Buhari zata fara ne daga misalin karfe 9 na safiyar Laraba zuwa karfe 3 na rana, don haka za’a rufe hanyoyin a tsakanin lokacin nan.

A wannan ziyara ta musamman da shugaban kasan zai kai, zai kaddamar da wasu manyan ayyuka akalla hudu da gwamnatin gwamna Akinwumi Ambode ya kammala.

Ayyukan da aka jera kamar yadda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya bayyana sune:

1. Gyararren hanyar Oshodi-Airport

2. Tsahar motar Oshodi

3. Sabbin manyan motocin haya 820

4. Sashen kula da mata mai gado 170 a asibitin LASUTH

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel