Ramadan: Limaman Saudiyya za su jagoranci sallar asham a kasashe 35

Ramadan: Limaman Saudiyya za su jagoranci sallar asham a kasashe 35

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa ministan harkokin addinin Musulunci na kasar Saudiyya, Abdullatif Al-Asheikh, ya yi na’am da batun tura kungiyar limamai 70 domin su jagoranci sallar asham da Tahajjud a kasashen duniya 35 a yayin azumin Ramadana.

Hakan dama chan al’adar ma’aikatar ne tura limamamaiu wasu daga cikin kasashen duniya a lokacin azumi domin jan salloli da kuma wa’azantar da Musulmai akan abun day a shafi addinin Islama.

Jaridar Saudi Gazeete ta rahoto ministan na cewa hakan wani sashi ne na kokarin masarautar don nuna kulawa da tallafawa dukkan musulmai a duk inda suke.

Ya ce limaman za su dora al'ummar musulmai kan turba ta gaskiya, su bayyana musu ainihin sakon musulunci na gaskiya su kuma wayar musu da kai kan duk abun da ya shafi rayuwar musulmi.

Ramadan: Limaman Saudiyya za su jagoranci sallar asham a kasashe 35
Ramadan: Limaman Saudiyya za su jagoranci sallar asham a kasashe 35
Asali: Getty Images

"An zabi malaman ne daga kwalejojin Shari'ah. Dukkansu mahaddatan Al-Kur'ani mai girma ne kuma masana sosai a addinin.

"Wadannan matasan malamai kwararrun masu wa'azi ne wadanda za su iya yi wa Musulmai bayanin addinin Musulunci sosai, kuma za su iya karanto Al-Kur'ani da ka," in ji shi.

Al-Asheikh ya ce masallatan kan cika makil da masu ibadah a lokacin azumi don haka babbar dama ce ga limaman su tafiyar da lokacinsu wajen amfanar mutane da wayar musu da kai.

KU KARANTA KUMA: Enang, Akpabio, da Udoma sun sa Buhari ya rasa inda zai sa kan sa

A ranar Litinin ne ministan ya gana da limaman ya kuma umarce su su zamo wakilai nagari ga kasarsu.

Ma'aikatar ta shirya musu wani taron karawa juna sani don kara wayar da kansu kan hanyoyin da ya kamata su bi wajen yada sakon musulunci a kasashen waje.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel