Rancenmu na nan a kashi 19 cikin dari na GDP, inji Ministar kudi

Rancenmu na nan a kashi 19 cikin dari na GDP, inji Ministar kudi

-Bashi bai yiwa Najeriya yawa ba har yanzu, inji Zainab Ahmad

-Masu amfana da tallafin man fetur ba yan kasuwa bane, a halin yanzu NNPC keda wannan alhaki

Ministar kudin Najeriya ta sahidawa yan kasar cewa bashin da ake bin Najeriya bai kazanta ba har ila yau. Inda take cewa kashi 19 cikin dari ne kawai na daga GDP, wanda yayi kasa dana kasashen Ghana, Brazil, Afrika ta kudu, Masar da kuma Angola.

A wani zance da ya fito daga bakin hadinmta, Paul Ella Abechi, ya kara da cewa ministar ta bada tabbacin cewa gwamnatin Najeriya bata da wani shiri na janye tallafin mai a daidai wannan lokaci.

Rancenmu na nan a kashi 19 cikin dari na GDP, inji Ministar kudi
Zainab Ahmad
Asali: UGC

KU KARANTA: A sirrance, a boye: An nada diyar Abba Kyari a matsayin mataimakiyar shugaba a hukumar NSIA

Kungiyar kudi ta duniya wato IMF, ta nemi Najeriya da ta janyen tallafin ne domin kawo karshen matsalolin da suka shafi ilimi da sauran ayyuka a kasar. Inda kungiyar ke cewa janye tallafin zai samar da kudaden yin wadannan ayyuka.

Ministar kuwa ta lura da cewa a halin yanzu, ba wai yan kasuwa masu zaman kansu ke amfana da tallafin ba “NNPC wacce ita ke shigowa da man ita ke rage farashin kana kuma ta mikawa gwamnatin abinda yayi saura.

“Hakan yafi kyau kwarai, domin ma yafi arha kuma a saukake za’a iya fahimtar me akayi ta hanyar bin diddigi,” a cewarta.

A bangaren rance kuwa cewa tayi, “Har yanzu muna nan a kashi 19 cikin dari na GDP, har ila yau rancenmu bai yi yawa ba. Abinda kuwa doka ta bamu dama ya kai shine kashi 25 na GDP. Idan kuwa aka hada kasarmu da sauran kasashe irin Ghana, Masar, Afrika ta kudu, Angola da Brazil zaka ga cewa mune masu karancin bashi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel