Yanzu Yanzu: Sarkin Katsina ya dakatar da hakimai 2
- Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya dakatar da hakimai biyu
- Wadanda aka dakatar sune Durbin Katsina, Hakimin Jikamshi, Alhaji Aminu Kabir Usman da Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin garin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman
- Sai dai babu wani bayani kan dakatarwar nasu a daidai lokacin wannan rahoton
Sarkin Katsina, mai martaba, Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya dakatar da hakimai biyu, kamar yadda shafin Taskar labarai ta ruwaito.
Wadanda aka dakatar sune Durbin Katsina, Hakimin Jikamshi, Alhaji Aminu Kabir Usman da Sarkin Sullubawan Katsina, Hakimin garin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman.
Ba a san dalilin dakatarwar nasu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton amma wata majiya da ba a tabbatar ba tace sakamakon wasu sabanin cikin gida ne.
An kuma tattaro cewa an dakatar da hakiman guda biyu ne yan kwanaki da suka shige amma dai masarautar bata saki wani bayani akan hakan ba.
Dakatattun hakiman sun kasance kanne ga sarki mai ci.
KU KARANTA KUMA: Gwamnoni, Ministoci na neman samun shiga a sabuwar Majalisar Buhari
A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gungun wasu miyagu yan bindiga marasa Imani sun yi awon gaba da wasu matan aure guda Tara da tsakar rana a kauyen Kuchi dake cikin karamar hukumar Munya ta jahar Neja a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a kokarinsu na yin garkuwa da matan auren, yan bindigan sun dirka ma wasu mutane uku bindiga, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar guda daga cikinsu, yayin da sauran biyun suka samu rauni.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng