APC: Sabon karancin albashin N30,000 dayane daga cikin alkawuranmu da muka cika

APC: Sabon karancin albashin N30,000 dayane daga cikin alkawuranmu da muka cika

-Buhari sanya hannu kan sabon karancin albashi na naira dubu talatin

-Ma'aikatan Najeriya sun samun karin albashin da suka dade suna jira

Jam’iyar APC mai mulki a halin yanzu ta jinjinawa Shugaba Buhari bisa ga sanya hannun da yayi akan sabon karancin albashin ma’aikatan Najeriya na naira dubu talatin. Babban sakataren jam’iyar na kasa gaba dayane ya fadi haka jiya a babban birnin tarayya.

Da yake jawabi sakataren mai suna, Mallam Lanre Issa-Onilu cewa yayi hakika wannan abu da shugaba Buhari yayi ya cancanci a yaba masa. Inda ya kara da cewa alkawarin da akayiwa yan Najeriya lokacin yawon neman zabene aka cika.

APC: Sabon karancin albashin N30,000 dayane daga cikin alkawuranmu da muka cika

Shugaba Buhari
Source: Twitter

KU KARANTA:Najeriya na kashe naira biliyan sha shida domin shigowa da wake –Gwamnatin tarayya

Issa-Onilu ya sake jinjinawa duk wandanda sukeyi ruwa da tsaki ganin cewa wannan abu ya tabbata kamar yanda yake a halin yanzu. Daga cikinsu kuwa akwai, Majalisar dokokin kasa, gwamnonin jihohi, kwamiti na musamman akan tabbatar da sabon tsarin albashin da kuma kungiyar yan kwadago ta kasa, tabbas sun taka rawar gani wacce ta cancanci a yaba masu.

“Ma’aikatan kasar nan ko shakka babu sun cancanci wannan karin na albashi. Musamman idan akayi duba ga matsalar tattalin arziki dake fuskantar kasar a wannan lokaci. Daya daga cikin abinda shugaba Buhari ke kokarin kulawa dashi shine jin dadin ma’aikata. Daga cikin wannan tsare-tsaren nasa akwai samar da muhalli ga ma’aikatan a fadin kasar nan.

“Hakika wannan kaddamar da sabon tsarin albashi da shugaba Buhari yayi, cika alkawarine yayi wanda ya furta lokacin yakin neman zabe.” Ya sake nanatawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel