Gobarar wuta tankar mai ta kashe direba da wata mata da goyo a jihar Oyo

Gobarar wuta tankar mai ta kashe direba da wata mata da goyo a jihar Oyo

-Gobarar tankar mai ta kashe mutane biyu a jihar Oyo ciki hadda mace da goyo

-An dauki kimanin minti talatin wannan wuta na ci kafin yan kwana kwana sun iso wannan wuri, inji wani wanda abin ya faru akan idonsa

Wani direban tasi mai suna Segi da wata mata mai dauke da goyo sun kone kurumus sakamakon kamawa da wuta da wata tankar mai tayi a gadar Samwill dake Onipepeye kan babban hanyar zuwa Legas daga Ibadan.

Direban ya fito daga motar tasa ne inda yake dibar man daya zuba a kasa daga wannan tanka yayinda wutar ta kama dashi. Ita kuwa matar tayi kokarin fita daga motar da take ciki amma abin yaci tura. Mijinta ne ke jan motar da take ciki wanda ya samu sa’ar fita tare da sauran yaransu biyu.

Gobarar wata tankar mai ta kashe direba da wata mata da goyo a jihar Oyo

Tankar mai na ci da wuta
Source: UGC

KU KARANTA:Najeriya na cikin matsanancin hali, OPC ta fadawa Shugaba Buhari

Wakilinmu ya bayyana mana cewa, wutar ta kai kimanin minti talatin tana ci kafin yan kwana kwana na jihar Oyo su karaso wannan wuri su da ma’aikatan hukumar kashe wutan na kasa.

Wani wanda abin ya faru a gabansa, mai suna Babatunde Ajayi ya shaida ma wakilinmu cewa da misalin karfe daya da rabi daidai lokacin da wutar ta fara ci za iya tsayar da ita.

Ga kuma abinda yake cewa: “Da misalin karfe daya da rabi, wata tankar mai dake hanyar zuwa Ibadan tayi kokarin kaucema haduwa da wata karamar mota a saman gadarta Samwill. Nan ne kuwa wannan mota ta kife a tsakiyan titi. Direban motan ya gudu ya bar wurin a daidai lokacin da wutar bata fara ci ba."

“Fetur ya fara bulbulowa daga cikin wannan tanka, a nan kuwa mutane suka fara rige-rige wajen dibar wannan mai kowa da jarkarsa. Har ma akwai wata mata wacce ta samu damar cika bokiti biyu da fetur. Wani direban tasi da yazo wucewa shima ya tsaya domin ya kwashi garabasa. A daidai lokacin da ya fara diban wannan mai ne sai tankin ya buga wuta kuwa ta kama. Sakamakon hakan wannan direban ya kone kurumus."

“Akwai wata mota kusa da inda abin ya faru, mutumin dake jaye da motar ya samu fita tare da yaransa biyu. Amma sai dai matarsa da ita da goyonta sun kone cikin wannan motar inda tayi yinkurin fita amma abin yaci tura.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel