Najeriya na kashe naira biliyan sha shida domin shigowa da wake –Gwamnatin tarayya

Najeriya na kashe naira biliyan sha shida domin shigowa da wake –Gwamnatin tarayya

-Najeriya na kashe kudade masu yawan gaske domin shigowa da wake

-Hanyoyin fasaha da kimiyyar zamani zasu taimaka wajen bunkasa noma wake a kasar nan, inji Bitrus Bako

Duk da kasancewar Najeriya itace kasa ta daya wurin noman wake a fadin duniya, amma hakan bai hanamu kashe makudan kudade ba domin shigo da wake kasar nan daga kasashen dake makwabtaka damu. Kudin da yakai naira biliyan goma sha shida.

Da yake magana wurin wani taro da aka shirya na sashen fasaha da bincike akan harkokin noma ranar Alhamis a Abuja, sakataren ma’aikatar kimiyya da fasha ta kasa wato Bitrus Bako cewa yayi, amfani da iri na waken da aka bunkasashi ta hanyoyin zamani na fasaha zai yi matukar taka rawar gani wajen noman waken.

Najeriya na kashe naira biliyan sha shida domin shigowa da wake –Gwamnatin tarayya

Nau'in wake
Source: UGC

KU KARANTA:Yan bindiga sun kashe mutum daya a wani kauye dake Jigawa

Bako, wanda daraktan ayuka na musamman ya wakilta mai suna James Sule ne ya bada wannan tabbaci inda yake cewa ingancin wannan wake da ya samu bunkasa ta hanyar zamani wanda za’a fara amfani dashi a shekarar 2020 zai kasance mai nagarta wajen ci da kuma kariya ta musamman daga barazanar kwari.

Kungiyar dake da hurumin samar da wannan iri na wake ta riga da ta bada izinin cewa a saki wannan waken a kasar nan. Hakan ne zai bada damar kawo shi kasuwanni domin kowane manomi ya samu damar mallakarsa kana kuma ya iya shukawa domin ya amfanesa.

Bako yace “Gabanin a fara amfani da wannan iri na waken mai inganci, manoma na amfani ne da maganin kashe kwari domin kariya ga waken nasu. Yin amfani da wannan maganin feshin na matukar cima manoman kudi kwarai da gaske, yayinda suka kasance suna sayen maganin feshin guda takwas ko ma sama da haka. A karshe kuma suna rasa kashi tamanin cikin dari na amfanin gonar tasu sanadiyar wadannan kwari.

“Abin zai yi matukar birgeku idan aka fada muku Najeriya itace kasa ta daya wajen noma wake a duniya, amma duk da haka abinda muke nomawar baya isanmu sai mun siyo daga wurin makwabtanmu irinsu kasashen Kamaru da Burkina Faso wanda ke ci mana kudi kimanin naira biliyan sha shida.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel