Najeriya na cikin matsanancin hali, OPC ta fadawa Shugaba Buhari

Najeriya na cikin matsanancin hali, OPC ta fadawa Shugaba Buhari

-Da dama daga cikin yan Najeriya suna rayuwane a cikin kunci

-Akwai bukatar Shugaba Buhari ya kawo dauki ga al'ummar Najeriya, inji jagoran OPC

Jagoran kungiyar yarbawa ta OPC, Oba Gani Adams ne yayi wannan kira ga Buhari cewa yayi kokarin ceto yan Najeriya daga halin da suke ciki a yanzu na kaka nikayi. Da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani a Ikeja ta jihar Legas yace yawancin yan kasar nan na ruyawane cikin kunci da kuma debe tsanmani.

Jagoran kungiyar ta OPC, da yake martani ga hadimin shugaban kasa, Femi Adesina yayinda yake tsokaci akan tattalin arziki kasar nan tun daga inda a fito izuwa halin da ake ciki a yau. Ya bada karfi ne fannin kawo cigaba ga mutanen kasar nan musamman talakawa ta yadda za’a sama masu ababen more rayuwa cikin sauki.

Najeriya na cikin matsanancin hali, OPC ta fadawa Shugaba Buhari
Gani Adams
Asali: UGC

KU KARANTA:Buhari zai kara kaimi a zango na biyu, inji wata Kungiya

Adams ya jinjinama wadanda suka hada wannan taro inda yake cewa ta wannan hanyar zasu iya aikawa da sako zuwa ga shugaban kasa ta hanyar hadiminsa. Akwai bukatar ace gwamnati ta fitar da sabbin tsare-tsare da kowa zai amfana a kasar nan.

Ga abinda jagoran yake cewa: “Dan uwana, Femi Adesina, yayi magana akan wasu matakan kasar nan a halin yanzu. Hakika yana yin aikinsa ne, domin haka ina so ka sanar da Shugaban kasa cewa Najeriya fa tana cikin matsanancin hali, daga dan abinda na sani. A nawa tunanin akwai bukatar Shugaban kasa ya duba wadanannan al’amura domin suna da matukar bukatar kulawa sosai.

Bari nayi amfani da kaina a matsayin misali bisa ga matsanancin halin da muka tsinci kanmu ciki a yau. Ina kashe sama da naira dubu goma sha uku a kullum domin zubawa injimin samar da lantarkin gidana mai. Kuma ko shakka babu wannan abune da yake faruwa a ko ina a fadin kasar nan. Hakan ne zai baka tabbacin cewa akwai matsala a fannin lantarki.

“Kididdiga da kuma hakikanin zance na nuna cewa har yanzu Najeriya da sauranta, indai har muna so ya kasance muna iya goga kafada da sauran kasashen duniya. Hakika gwamnati tayi matukar kokari akan tattalin arziki kamar yanda Adesina ya fadi. Sai dai akwai bukatar sake bunkasa tsarin tattalin arzikin namu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel