Lafiya uwar jiki: A ci gishiri kadan domin inganta lafiya

Lafiya uwar jiki: A ci gishiri kadan domin inganta lafiya

-Cin gishiri mai yawa na haifar da matsololin da suka shafi ciwo hanta, koda da kuma hawan jini

-Ba wai dandanon abinci ba, a kula da mai za'aci domin karin lafiyar jiki

Shugaban kamfanin ‘Tropical Investment Group’ mai suna Dakta Onyekachi Onubogu ne yayi wannan kira ga yan Najeriya, inda yake cewa a rage cin gishiri da yawa domin hakan na iya haifar da cutar hanta.

Onubogu ya fadi hakan ne a Legas yayinda yake gabatar da sabon sinidarin karawa abinci dandano mai suna Terra Cube, inda ya sake cewa ya zama wajibi mu kula da yawan gishiri a cikin abincinmu ko dan mu gujewa cutar koda da kuma hawan jini.

Lafiya uwar jiki: A ci gishiri kadan domin inganta lafiya

Lafiya uwar jiki: A ci gishiri kadan domin inganta lafiya
Source: UGC

KU KARANTA:Buhari zai kara kaimi a zango na biyu, inji wata Kungiya

“Bana tunanin cutukan koda nada wata alaka da sinidarin karawa abinci dandano, amma sai dai daya daga cikin abinda da dama cikin yan Najeriya suke fada shine suna da bukatar su rage gishiri cikin abincinsu. A don hakane muka tabbata mun rage gishiri a cikin wannan sabon sinadarin namu kasa ga wadanda ke kasuwa a yanzu.

“Ba wai karawa abinci dandano bane kadai abin lura, amma kaci abinda ba zai taba lafiyar jikinka ba shine abin dubawa. Domin masu iya magana na cewa: Lafiyarka jarinka.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel